Yadda Za Ki Hada Banana With Mango Juice Na Musamman

Yadda Za Ki Hada Banana With Mango Juice Na Musamman
*Zee Sabo kitchen*
 
 
 
 
 Banana With Mango Juice  
 
Abubuwan buqata
 
1_Ayaba
2_Mangwaro
3_Kamshi
 
Yadda za'a hada
 
Za'a bare Ayaba a cire bakin dake tsakiyarta sai a yanka ta kanana, shi ma mangwaro za'a gyarashi a cire fatar sai a yanka wannan naman  Mangwaron a hada da Ayaba  a markada a zuba ruwa ba da yawa ba, sai a juye a tace , a saka suga da kamshi shikenan.
Akwai matukar amfani da yawa mace ta rika hada kayan sha irin na marmari da kanta domin kula da lafiyar jikinta da kuma ta iyali.
Sinadaran da ake sanyawa Juice na kwali da kwalba da roba domin hana su lalacewa tsawon lokaci masana na ganin suna kawo cikas ga ingantuwar kiyon lafiyar jiki, don kaucewa hakan nake ganin matukar dacewar rika hada naka da za ku sha nan take ba tare da kun sanya wasu kayan kashe tsami ko daidata zaki ko hana lalacewa ba.
Hada lemu na asali ba wani kala yana da armashi a wurin iyali har dai in hadi ya ba da hadin kai ga mace.