Alawar Madara
Madara gwangwani biyu,
Sugar cokali biyu,
Ruwa kwatan kofi,
Flavor karamin cokali daya,
Butter cokali daya,
Zaki zuba sugar a tukunya saiki ki sa ruwa sai ki zuba butter ki zuba flavor ki barshi ya dahu saiki kashe ki kawo madarki ki zuba ki juya sosai saiki juyeta a Leda ki yanka ko Kuma ki mulmulata idan Kinada cutter kiyi irin shape Dinnan.
Alawa kayan marmari ce da uwar gida kan yi don burge iyalanta.



