Yadda Za Ki Haɗa MIYAN GANYE Mai Daɗin Gaske

Yadda Za Ki Haɗa MIYAN GANYE Mai Daɗin Gaske

Abubuwan da ake bukata:

Ganyen ugu
Ganyen shuwaka
Ganyen Gauta
Ganyen gure
Nama
Kifi
Tattasa/ tarugu
Daudawa
Maggi/spicy
Manja

Yanda zaki hada:

Zaki wanke nama ki saka magi da albasa ya dahu,sai ki yanka ganyen ki duka ki wanke, ki Nika kayan miyan ki ba da tumatur ba, Sai ki wanke kifin ki ki aje gefe. Idan nama ya dahu Sai ki zuba manja, da kayan miyan da maggi daidai dandanon ki, ki saka daudawa, ki zuba kifi, Sai ki rufe ki barshi ya gisdu kadan, sannan ki fara zuba ganyen Gauta domin yafi sauran ganyen karfi ya Dan dahu na minti 5 Sai ki zuba sauran ganyen.

Kada a manta bamu saka ruwa ba ruwan tafashen nama ne kawai mukayi amfani da shi Sai ruwan da ke cikin ganyen. Idan ya dahu Sai ki sauke.

Zaki iya ci da kowane irin tuwo, ko shinkafa.

Kuma ana hadama masu fama da matsalar jini a jiki.

Tested nd trusted 

Daga Safiya Usman