Yadda Za Ki Haɗa Alkaki Na Musamman

Yadda Za Ki Haɗa Alkaki Na Musamman
Yadda Za Ki Haɗa Alkaki Na Musamman 
2 cups alkama
340g yoghurt
2 tbsp oil 
2 cups sugar 
2 and half cup of water lemon
Yadda ake yi
Na ɓarza Alkama cikin blander na barxa kar ta yi laushi sosai da dan tsaki yafi, bayan na gama sai na juye cikin bowl nasa mai na juya Sosai bayan sun hade saina xuba yoghurt dina ina xubawa ina juyawa harta hade ta kame jikin ta,saina rufe tsawon awa daya,zan ga ta kara kame jikin ta,tayi karfi sai na fara yayyafa mata ruwa ina kara bugata ina yayya fawa har tayi min yanda nakeso tana bukatar bugu saboda, ta  hade ba tare da ta bada matsala wajan nadi ba,bayan kin tabbatar ta hade saiki nadata yanda ake nadin alkaki shikenan sai ki soya wuta sama sama saboda cikin ma ya soyu,yana soyuwa saiki kwashe ki xuba cikin sugar,
Shikenan alkaki ya kammala,
Yanda na dafa sugar zaki zuba sugar، ruwa cikin tukunya saiki matse lemon a ciki ki barsu harsu fara kunfa yayi danko shikenan sai a kashe wutar, kina iya amfani da ruwan tsamiya amaimakon yoghurt,idan baki jure bugu ki xuba cikin mixer kou turmi in sha za'a gane wannan bayani nawa typing wahala.