Yadda Za Ki Gyara Jiki Da Carrot

Yadda Za Ki Gyara Jiki Da Carrot
 
 

Carrot waton Karas dai kamar yadda kowa ya sani yana cikin kayan marmari na lambu da ke inganta lafiyar jikin dan adam,  mafi akasari ma wadansu su kan yi amfani da shi wurin gyaran fata, domin samun lafiyar fata da jiki mai kyau da ƙyalli.

Hanya ta farko:
 
'Yar uwa idan kina son fatar jikinki ta yi kyau mai inganci da ɗaukar idanuwa maza ki yawaita cin carrot akai akai.
 
Hanya ta biyu:
 
Ki dinga goga carrot a magogi sai ki matse ruwan ki zuba a roba saiki samu audiga ki dinga dangwalata cikin ruwan kina gogawa fuskarki da shi kafin ki shiga wanka.
 
Na baki sati ɗaya Ƴar uwa, tabbas za ki sha mamaki.
 
DOCTOR MARYAMAH. managarciya.com   

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow

News paper