Yadda Aka Yi Bidiyon Tsiraicina Ya Fita--- Safa Mawakiya

Yadda Aka Yi Bidiyon Tsiraicina Ya Fita--- Safa Mawakiya

 

Korarriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan hausa, Safiyya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta shirin Kwana Casa'in ta magantu a kan sallamarta da kamfanin Arewa 24 ta yi. Safa kamar yadda ake kiranta a yanzu ta bayyana cewa wasu na kusa da ita ne suka fitar da bidiyon domin ta kan yi su ta ajiye a cikin wayarta idan tana jin nishadi. 

Tsohuwar jarumar wacce ta zama mawakiya a yanzu ta kuma bayyana cewa farkon faruwar abun sai da ta kwashe tsawon watanni uku bata fita ba saboda kunyan mutane.
A hira da ta yi da sashin Hausa na BBC, Safa ta ce ta fuskanci tarin kalubale tare da la’anta a wajen mutane wadanda suka yi zargin cewa ita yar madigo ce ko kuma saurayi ta turawa ya fitar da shi. 
Hakazalika ta ce ya kai har wani ya jefeta da dutse a layinsu wata rana da ta fito waje, kuma cewa haka ake ta tsine mata a shafukan soshiyal midiya har ta kusa share shafukanta na Instagram, TikTok da sauransu. 
Sai dai kuma, Safa ta ce ta dawo daidai ne bayan iyayenta da danginta sun karfafa mata gwiwa tare da nusar da ita cewa hakan kaddara ce a rayuwarta, kuma ga shi a yanzu komai ya wuce.