Managarciya

Ya kashe Makwabcinsa kan Jalkar Ruwa a Sokoto

Wani matashi Ibrahim Baba  ya kashe maqwabcinsa Abubakar Ahmad kan matattar jalkar ruwa a titin Ubandoma unguwa Sabon titi cikin binin Sakkwato.

Qanen Margayi Umar Ahmad ya ce yayan nasa ya bar mata xaya da yara biyu, matar da tsohon ciki, “rasuwarsa ta faxo mana kwatsam ba mu za ta ba, abin da ya faru bama tsammanin ya kai ga yin kisa na gilla haka, magayin ya xauki wata matattar jalka ta maman yaron da aka bari wuin xibar ruwa sai ya yanke samanta ya yi amfani da ita, daga baya ta samu labari ta nemi ya biya ta ya aminta da haka zai ba ta 1500 ta ce ba ta buqatar su, rigima ta kai in da qanen mahaifinmu ya ce zai biya ta ce dole sai wanda ya xauki jalka ne zai biya, a haka ta faxawa xanta Baba.

“A ranar Laraba da tsaka dare margayin ya fito waje zai yi fitsari ashe matashin da abokansa suna jiran fitowarsa anan fa ya buga masa kokara a kai ya faɗi ya sake buga masa a zuciya, da suka tabbatar ya mutu, suka jefa shi a cikin makarantar Islamiyya, daga nan ya tafi ya sanar da mahaifiyarsa ya buge wane kan Jalkar da kika faɗamin anan ta ce masa ya gudu, ita ma ta gudu, ba wata hatsaniya a tsakani kan jalka ne kawai.”

Ya ƙara da cewar wanda ya yi haka maƙwabcinmu ne, sun zargi mahaifiyar yaro da hannu wurin kisan ɗan uwansu don haka za su jira su ga abin da doka za ta yanke kan jinin ɗan uwansu.

Malam Rufa’i Alhaji Sama’ila Rungumi ya ce abin da ya kawo kisan ba taka kara ya karya ba, yaro ne matashi dake sana’ar wankin babura da motoci don ya samu abin da ya ci a sana’ar ne ya ɗauki wata jallaka ya yanke, mai ita ta ce sai an biya ta aka ce za a saya mata sabuwa ta ce ina ba a biya ba za ta sanar ɗanta shi kuma yaro ne da bai jin magana, da ta gaya masa ne shi kuma ya ɗauki wannan mataki.

Ya ce matasan sai suka ɗauko wanda suka kashe suka ɓoye shi a ajin da ke cikin makarantar mu, a binciken da ake yi aka ga margayin, “ana ganin haka aka sanar da jami’an tsaro bayan sun zo aka tafi da gawar asibiti a can aka tabbatar kisan gilla ne aka yi masa.”

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Sakkwato DSP Rufa’i Ahmad duk yinƙurin jin ta bakinsa ya ci tura.

Exit mobile version