Home Rahoto Ya harbi saurayi da baka don ya ganshi da matarsa a...

Ya harbi saurayi da baka don ya ganshi da matarsa a Yobe

18
0

Ƴan Sandan Jihar Yobe sun cafke wani matashi mai shekaru 22 da ake zargi da harbin wani matashi da kwari da baka a Danewa Biriri da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar.

Ya ce, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya tarar da matarsa da matashin a kusa da gidan iyayenta a wani yanayi da bai gamsu ba.

Sanarwar ta ce, rikicin da ya biyo baya ne ake zargin ya harbi mutumin da kwari da baka, lamarin da ya jikkata shi.

Rundunar ta ce, wanda aka jikkata na karɓar magani a Asibitin ’Yan Sanda da ke Damaturu, yayin da wanda ake zargin ke hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here