Home Labarai Ya ɗauki nauyin yarinyar abokinsa ya yi wa ciki har ta...

Ya ɗauki nauyin yarinyar abokinsa ya yi wa ciki har ta haihu a Zamfara

12
0

Wani mutum ya ɗauki nauyin ɗawainiya da budurwa ’yar shekara 22 da ta ce abokinsa ne ya yi mata ciki, har zuwa lokacin da za ta haihu a Jihar Zamfara.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Hisbah ta Jihar Zamfara, Umar Haruna Tsafe, ya fitar.

Sanarwar ta ce, jami’an Hisbah sun samu budurwar tana ɗauke da cikin wata tara a wani gida da ke Gida Dari a Gusau.

Budurwar ta shaida wa Hisbah cewa wani matashi ne ya yi mata cikin, sannan daga bisani ya tsere ya ƙyale ta.

Sanarwar ta ce, Hukumar ta gayyaci abokin matashin, wanda ya amince zai ɗauki nauyin tallafa wa budurwar da kula da ita har zuwa lokacin da za ta haihu.

Hisbah ta kuma tuntubi mahaifinta, wanda ya ce ya taɓa yafe wa ’yar tasa, amma ya umarce ta da ta bar masa gida, kuma an taɓa kai batunta gaban Hisbah har sau biyu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, wata mata mai suna Sadiya Shehu Gusau ta amince ta karɓi budurwar domin zama a wurinta,

Hisbah ta ce, yayin da take tsaka da tattara rahoto kan lamarin, budurwar ta fara nakuda, inda yanzu haka jami’anta suka garzaya da ita asibiti domin samun kulawar lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here