WATA UNGUWA:Fita Ta 26

WATA UNGUWA:Fita Ta 26

BABI NA ASHIRIN DA SHIDA

 

 

Cikin hanzari Sorfina ta ƙarasa wurin tare da janye Mahee daga wurin ba tare da ta ce komai ba.

Alhaji ya biyo bayansu a cikin mall ɗin yana faɗar "Haba don Allah! Ya zaki janye ta muna magana?"

 

Sorfina ta yi kicin-kicin da fuska ta juyo ta fuskance shi.

"Ka ga Alhaji, wannan ba irinsu ba ce ka yi haƙuri ka daina binmu a baya."

 

Murmushi ya yi ya ce "Haƙuri dai zaki yi 'yar budurwa, ni ina raɓarta ne da alkhairi bai kamata ki saka kafa ki ture wannan gingimemen alkhairin dake tunkaro ku ba."

 

Ta saki fuska tare da yin fari da ido "Shi kenan, mu yanzu siyayya muka zo muna sauri ne bari na baka numberta sai ku yi magana daga baya."

 

Har zuwa lokacin Mahee ba ta ce komai ba sai binsu take da ido.

Alhajin ya karbi number tare da faɗar "Wane suna zan saka ne?"

 "London girl." Ta faɗa tana rage murya tare da watsa mishi wani irin kallo.

Murmushi kawai ya yi a ransa ya ce 'Wannan tana so ta ɓata mini shiri, amma bari na kwaɓar da wasar kawai.'

 

Ko da ya ɗago har sun ƙara gaba suna ɗibar kayayyakin da suke so, bayan wani ɗan lokaci suka gama siyayyar suka tura basket ɗin zuwa wajen da ake biyan kuɗi.

 

Manyan alhazan dake wurin sai kallon Mahee suke suna haɗiye yawu, a wurin biyan kuɗin suka sake haɗuwa da Alhajin ɗazu, ya kalli mutumin dake girka kuɗin ya ce "Nawa ne kuɗin da suka kashe duka?"

"250,000 dubu ɗari biyu da hamsin."

Ya gyaɗa kai tare da saka hannu a aljihu ya zaro Atm card ɗinsa ya miƙa masa, ba musu ya karbɓ ya ciri kuɗinsa.

 

"Sunana Alhaji Rabi'u ni ɗan majalisar tarayya ne na nan jihar, na manta ban gabatar maku da kaina ba. Ke fa ya sunanki?"

 

Ya faɗa yana kallon Maheerah yayin da suke tunkarar ƙofar fita daga mall ɗin, da kamar ba zata yi magana ba sai can ta ce "Mahee."

'Sai dai ka faɗa mata ita dake ɓakuwa a garin, amma fa ni ai na fi kowa saninka ni da ke da plan a kanka.' Sorfina ta faɗa a ranta tana satar kallon shi.

 

A dai-dai lokacin suka zo ƙofar fita Sorfina ta kalle shi "Mun gode Alhaji ya kamata mu rabu daga nan."

Ta ja hannun Mahee suka fice da sauri.

A boot aka saka masu kayansu suka shige motar Fu'ad ya fisge ta da ƙarfi ba tare da ya ce masu kanzil ba.

 

Bayan komawarsu gida, Sorfina ta hau zirga-zirga a ɗakinta tana tunani "Inah! Ba zai yiwu ba, ba zan bari ki lalata mini buri daga shigowarki rayuwata ba, zan san yadda zan yi na kwaɓar da tunaninsa daga kanki Mahee.'

 

Ta zauna gefen gado tana huci "Fu'ad ne ya shiga tsakani na da wannan burin, dole zan san yadda zan yi na tura shi zuwa ƙololuwa ta yadda zai yi nisan kiwo har na kammala cika burina ba tare da ya lalata mini shiri ba."

 

Ta miƙe ta shiga banɗaki ta sakarwa kanta ruwa masu ɗumi, sannan ta fito tana saisaita nutsuwarta, ta sake shirya wa cikin ƙananun kaya ta fita zuwa ɗakin Maheerah.

Knocking ƙofar ta yi "Shigo" Mahee ta karɓa mata daga ciki, ta shiga da murmushi ta zauna kusa da Maheerah a gefen gado.

 

"To ya kika ga garin namu?"

"Ah! gari ya yi kyau sosai, da ma ina jin labarin Babban birni yau sai gani a cikinsa."

 

"Madallah! Yanzu ɗauko ledojin kayan can mu sake dubawa."

Mahee ta miƙe ta ɗauko kayan suka fara baje su akan gadon.

 

Sorfina ta ɗauko wata ɗangalalliyar riga mara hannu, wacce ta ƙoshi da adon stones ta kalli Mahee "Wow! Sis kalli wannan rigar, ba ƙaramin kyau zata miki ba idan kika saka."

 

Mahee ta kalli rigar sannan ta kalli jikinta, sai ta hau ƙanƙame jiki da hannuwa.

"Me ya faru?"  Ta tambaya da mamaki.

"Gaskiya sister ina ga ba zan iya saka wannan rigar ba ko alama, waɗannan ma da suke jikina da ƙyar na iya fita da su, duk wani iri nake ji."

 

Sorfina ta shiga naɗe rigar tana harhaɗa sauran kayan "Ai shi kenan, sai ki haƙura da cika burinki domin ina ga ba zai taɓa cika ba."

 

Cikin rawar baki ta ce "Ka...mar ya na haƙura da bu...rina? Kin san me kike faɗa kuwa?"

 

Sorfina ta yi mata wani irin kallo ta haɗe fuska alamun ba wasa ta ce

"Eh mana, idan har ba zaki iya saka wannan kayan ba, banga dalilin da zai saka ki ɗauki rayuwar bariki a matsayin hanyar cikar burinki ba."

 

Mahee ta kafe ta da ido kawai "Ba zancen kunya a cikin wannan harkar, idan har kina son mu yi wannan tafiyar dake dole sai kin cire rigar kunya kin yafa mayafin rashinta, sai kin ƙulla alaƙa da ɓata garin mutane sa'annan ne zaki samu riba biyu."

 

Ta ɗan yi shiru tana kallon Maheerah sannan ta ɗora "Riba ta farko zaki tara kuɗaɗe marasa adadi da zaki iya cika duk wani burinki da su, riba ta biyu zaki cimma burin da ya fito dake duniya."

 

Maheerah ta gyaɗa kai cikin gamsuwa "Na yarda dake sis, ki ɗora ni akan hanya, domin ba zan taɓa yada wannan burin ba duk rintsi bana jin kuma akwai wanda zai iya dakatar da ni."

 

"Da kyau yanzu kika ɗauki hanya." Ta faɗa fuskarta da fara'a.

 

************

Irfan kuwa bayan fitowarsa daga gidansu Maheerah kai tsaye office ɗinsa ya wuce, bayan ya zauna akan kujerarsa ya kira yi ɗaya daga cikin yaransa na wurin aiki a waya, bayan cikar minti uku sai ga shi ya turo ƙofar da sallama a bakinsa.

"Sir gani." Ya faɗa yana gyara tsayuwarsa a gaban Irfan.

 

Irfan ya ciro wata 'yar takarda a aljihunsa ya miƙa masa "Salis karɓi wannan takardar, ka je wannan address ɗin ka bincikar mun waye Ja'afar (Jafsee), ina son sanin komai da komai game da shi hope ka fahimce ni."

 

Ya gyaɗa kai "Yes sir, na fahimta."

"Hurry up."

"Ok sir."

 

Ya juya lokacin da yake saka takardar a aljihun gaban rigarsa ya fice.

Irfan ya fesar da iska daga bakinsa tare da dafe kansa da hannu biyu, ya ba wa kujerar da yake kai amana ta hanyar jinginar da kansa a jikinta.

 

'Ni da kaina ya kamata na je wurin nan, amma na sani dokin zuciya zai iya fisga ta na aikata ɗanyen aiki, wanda haka zai iya sakawa baya ta haihu.'

Ya miƙe tsaye ya shiga kaiwa da komowa yana faɗar

"Wannan yaron ya cuce ni, ya nisanta ƙwayar idona da kallon wacce ke sanyaya zuciyata. Idan har ta tabbata cewa yaudararta ya yi ni kaina bansan hukuncin da zan yanke masa ba."

 

Ya yi huci yana juyar da kai, "Ba wannan ya kamata na fi damuwa da shi ba, neman matata shi ne mataki na farko da ya kamata na bi."

 

Yana gama faɗa ya kwashi key ɗin motarsa da wayarsa ya zuba a aljihu ya bar office ɗin cikin hanzari.

Dai-dai zai fita suka ci karo da Ma'eesh.

Da mamaki ya kalle shi "Saurin me kake yi haka Irfan? sai ka ce wanda zai tashi sama?"

 

"Gidajen yaɗa labarai zani, zaka raka ni ne?"

"Me zaka yi a can?" Ma' eesh ya tambaya.

Irfan ya ci gaba da tafiya akan duga-dugansa yana faɗar

"Malam ka adana tambayarka sai na dawo, ni ka ga tafiyata."

Ya ƙara saurin tafiyarsa, cikin hanzari Ma'eesh ya bi bayan shi domin yana tsoron Abin da zai je ya dawo, idan har ya bar shi ya tafi shi kaɗai to fa sai yadda ta yiwu wai naƙuda a ɗakin mayya.

 

 

Ummu Inteesar ce