WATA UNGUWA: Fita Ta 41

Mahee ce take ta wannan zancen zuci yayin da take tsare a cell. Mamaki duk ya gama mamaye ƙwaƙwalwarta, tana mamakin wannan al'amari ainun, duk tarin alhazawan da take da su an kasa samun ɗaya da zai zo ya yi belin ta duk cikin waɗanda aka kira. Kowa da uzurin da yake bada wa, haka ƙawayen cin mushenta waɗanda suka ƙara zuga ta, ba wacce ta zo da nufin duba ta, bare ta saka ran za su taimake ta, ga shi yanzu har ta kwashe tsayin makwanni biyu a tsare.

WATA UNGUWA: Fita Ta 41

BABI NA ARBA'IN DA ƊAYA

 

A haka suka ingiza ƙeyarta zuwa motar su, suka tafi da ita.

Tun a motar take mamakin abin da ta yi aka je har gidanta aka yo mata kamun wulaƙanci haka.

Bayan isar su Station ne ta ji cewar wai ana tuhumar ta ne da laifin cin zarafin baƙinta su uku har ma hakan ya yi kusan sanadiyyar ran ɗaya daga cikin su. A nan farashin tashin hankalinta ya ƙara hauhawa.

 'Wannan fa shi ake kira tsautsayi auren shiɗaɗɗe. Ina zaman zamana lafiya na gayyato wannan baƙuwar masifar zuwa gidana. Na manta cewa Ja'afar bai taɓa zama silar alkhairi a rayuwata ba sai dai akasin hakan.'

Mahee ce take ta wannan zancen zuci yayin da take tsare a cell. Mamaki duk ya gama mamaye ƙwaƙwalwarta, tana mamakin wannan al'amari ainun, duk tarin alhazawan da take da su an kasa samun ɗaya da zai zo ya yi belin ta duk cikin waɗanda aka kira. Kowa da uzurin da yake bada wa, haka ƙawayen cin mushenta waɗanda suka ƙara zuga ta, ba wacce ta zo da nufin duba ta, bare ta saka ran za su taimake ta, ga shi yanzu har ta kwashe tsayin makwanni biyu a tsare.

 

Mutane biyu ne suka fi ba ta mamaki a cikin wannan al'amarin, Alhaji Rabi'u da Sorfina kwata-kwata ba ta yi tsammanin haka daga gare su ba, a zatonta ko da kowa zai juya mata baya a rayuwar bariki su biyun nan ba za su taɓa iya watsa mata ƙasa a ido ko su guje ta ba, sai ga shi tun ba a je ko'ina ba ta gano hakan. Sai a lokacin ta hango girman kuskurenta na fantsamowa bariki da ta yi. Duk da har yanzu ba ta daina jin haushin Abbanta ba a kan hukuncin da ya yi mata, kuma ba ta ajiye mummunan burin da take son cikawa ba.

 

Tana cikin wannan halin ne aka buɗe ƙofar cell ɗin da take "Ki fito kina da baƙuwa a waje?" Cike da mamakin wanda ya zo ta bi bayan 'yar sandar suka isa bakin kanta.

 

Zuly (aminiyar Sorfina) ta gani tsaye tana faman tauna cingam.

Ta dinga jefa wa Mahee kallon wulaƙanci kafin daga bisani ta yi 'yar dariyar mugunta, kana ta saka hannu a jakarta ta janyo wata farar takarda ta miƙa wa Mahee tana faɗar

 

 "Sakonki ne daga Bestie, kin ga tafiyata, ba zan iya haɗa numfashi da ke ba."

Mahee ta kalle ta da mamaki,

"Zuly! Yanzu ni ɗin ce kike cewa ba zaki iya haɗa numfashi da ni ba? Kada ki manta har magiya kike yi mini don ki zauna tare da ni..."

Ba ta bari ta ƙarasa ba ta katsi numfashinta da faɗar "Ada kenan, amma a yanzu kin duba fuskarki a madubi kuwa? Ko karen bariki ba zai 'yarda ya biyo ki ba a dai irin yadda kika lalace kika ƙarjame ɗin nan. Kodayake karɓi wannan shi ne dalilin zuwana."

Mahee ba ta karɓa ba sai ƙamewa ta yi giyar mamaki na ɗawainiya da ita.

Da Zuly ta ga hakan sai ta ajiye mata takardar a kan kantar ta juya.

'Yar sandar ta buga mata tsawa da cewa ta ɗauki sakonta ta koma cikin cell.

 

Haka ta ɗauka ta juya jiki ba ƙwari ga wani irin jiri da ya fara kwasar ta. Bayan ta zauna ta warware takardar ta fara karantawa kamar haka

 

Dear Sis

  Wannan wasiƙar gaisuwa ce, jinjina tare da fatan kina cikin walwala a yanayin da kike, da fatan yanayin wajen ya yi miki daɗi domin idan har Ja'afar ya rasa ransa, gidan kurkuku ne zai zame miki muhalli na har abada koma a salwantar da ranki baki ɗaya. Kuma ina sanar da ke cewa har yanzu Ja'afar yana cikin jihar nan yana jinya a asibiti. Na san zaki yi mamaki rashin zuwana gare ki a cikin wannan hali, to amma idan kika tuna rayuwar da ta haɗa mu ba abin mamaki ba ne, rayuwar barikin da ma ba ta mutunci ba ce.

Dalilin rubuto wannan wasikar ina son na bayyanar miki da ɓoyayyen sırrın da baki san shi ba, kuma wanda zai jijjiga ki.

Ni ce nan na shirya tuggun da aka tare motar su Ja'afar, tare da haɗin bakin su Tukur, idan Ja'afar ya mutu ke za a tuhuma kuma iyayensa za su yi shaida akan hakan.

Na san yanzu haka guguwar mamakin dalilin da ya saka na yi hakan tana wujijjiga ƙwaƙwalwarki, to sauraren ni ki ji.

Na yi haka ne saboda kin shigo rayuwata kin fi ni samun ɗaukaka a harkar da ni ce na ɗora ki a kai, uwa uba kin ƙwace Alhaji Rabi'u da tun lokacin da na fara harkar bariki nake farautarsa, dukiyarsa nake so na ga na mallake ido a buɗe kafin daga bisani na hallaka shi kamar yadda shi ne silar raba ni da darajata a matsayina na ya mace. Wannan shamakin da kika yi mini a lokacin da na kammala shirye-shiryena na samun shi a hannu ya saka na shirya miki wannan tuggun.

Wani labarin da baki sani ba kuma shi ne Yanzun haka Alhaji Rabi'u ya shigo komata, tuni ya manta da rayuwarki, kuma ba wanda ya isa ya mini shamaki ga cika burina akansa.

     Mai ƙaunarki Sorfina London girl

 

Tana zuwa nan a karatunta ta ja wani malamin tsaki yayin da ƙwallar takaici ke sauka a kumatunta.

Ta shafa cikinta tana faɗar "Da nasan haka bariki take da ban yi wannan cikin don na baƙantawa iyayena ba, ka yi haƙuri babyna na samar da kai ta kazantacciyar hanya, sai dai duk lalacewa ta nasan girman zunubin kisa, saboda haka ba zan iya zubar da kai ba."

Ta faɗa cikin raunanniyar murya da sautin kuka.

 

Nan take nadamar rayuwa ta shige ta, sai a lokacin ta tuno ita 'yar malamai ce ta fara jero duk addu'ar da ta zo bakinta, tana neman Allah ya Kawo mata mafita a cikin wannan al'amarin.

 

@@@@@

 

Irfan kuwa tunda ya samu kira daga Maisha, jiki na ɓari suka je shi da Umar suka same ta har hotel ɗin da ta yi musu bayani.

Isar su hotel ɗin ke da wuya ta fito cikin harabar hotel ɗin tana karairaya ta je har gaban motar su, sai ta buɗe gidan baya ta shiga.

Bayan sun gaisa ne ta kora musu bayanin duk abin da ta sani game da Mahee da abin da suka aikatawa Jafsee da iyayensa har ma da kama tan da yan sanda suka yi. Suka yi mata godiya tare da cake mata kuɗin da suka alƙawarta wa wanda ya kawo labarin ta fice daga motar.

Da ma Umar ne ke jan motar kasancewar shi ne ɗan gari ya san kowane lungu da saƙo na jihar.

Suna barin hotel ɗin Umar bai zame ko'ina ba sai station ɗin da aka kai Mahee.

Tun ma Umar bai daidaita tsayuwar motar ba Irfan ya fito da hanzari ya fara nufar kofar da yake zaton za ta sada shi da cikin station ɗin.

Umar na gama gyara fakin ya bi bayansa a hanzarce, suna zuwa bakin kanta suka tarar da kofur Bala, shi suka yi wa bayanin abin da ya kawo su.

 

Kofur Bala ya yi musu iso a wurin d.p.o bayan sun gaisa Umar ya shiga koro bayani "Ranka ya daɗe sunana Umar Tahir Bega, ni ɗa ne ga sanata Tahir Bega na zo nan ne tare da abokina muna neman belin ƙanwarsa da kuka kama, fatan za a yi mana wannan alfarmar."

D.p.o ya ɗan karkaɗa kai alamar ya fahimci zancen kafin ya ce "Ai yallaɓai don wannan ma ko aike ka yi, in dai abin bai fi karfinmu ba sai mu iya ba da belinta. A dai girma da karamci irin na mahaifinka ba taimakon da ba zan iya yi wa zuri'arsa ba, sai dai wanda yafi ƙarfina."

Ya ɗan tsagaita kafin ya ce "Ya ne sunanta? Wane laifi ta aikata."

 

Irfan ya yi karaf ya ce "Sunanta Maheerah Isah idan dai ba canza sunan ta yi ba, wadda ta labarta mana ta ce wai an kamata ne da tuhumar cin zarafin tsohon saurayinta da mahaifa sa har shi saurayin ya kusa rasa ran shi."

Ya faɗa fuska ba walwala.

D.p.o ya shiga duba wasu takardu da ke gabansa can ya ɗago ya ce "Ba wata Maheerah Isah a nan, ga dai wata karuwa mai suna Maheeluv da yaranmu suka kamo sati biyu Baya, kyas ɗin su iri ɗaya da wacce ka ambata yanzu."

Lokacin da Irfan ya ji ya ambaci abar ƙaunarsa da karuwa sai ya ji tamkar ya caka masa wuƙa a ƙahon zuci, sai dai ba shi da abin da zai iya yi domin ita ta zaɓawa kanta wannan sunan.

 

D.p.o ya kira Sajen Bala ya masa umurnin ya je ya fito da Maheeluv ya zo da ita, don baƙin su duba ko ita ce.

Ba musu ya je ya buɗe cell ɗin tare da rakiyar wata yar sanda mace Mahee ta sako kai cikin office ɗin kanta na sunkuye a ƙasa.

Ƙarar Turo ƙofa ya saka a hanzarce suka juya su duka biyun suna kallon ƙofar shigowa.

Irfan ya zabura ya miƙe da hanzari yana ƙare mata kallo. Tabbas ita ce domin ko a mafarki ya ganta zai shaida ta, bare ba baƙi da yar ramar da ta yi ya ƙara maidata sak Maheerar da ya sani a baya.

Ƙare mata kallo kawai yake har suka iso kusa da shi, tuni idanunsa suka kaɗa suka yi jazir ganin irin shigar da ke jikinta, ya ƙara tabbatar da zancen Hanif da na sauran jama'a cewa ita mai zaman kanta ce, bai san lokacin da ya ambaci sunanta da ƙarfi ba.

"Maheerah! Maheena!!"

 

Sai a lokacin ta ɗago kanta saboda jin sautin da take da yaƙinin ta yi sabo da saurarensa duk da ta manta ko a'ina ne, ta kalli sashen da sautin ya fito. Magananta suka sauka a kan fuskar da ba za ta taɓa manta taswirarta ba har gaban abada.

Cikin barin baki ta ce "Ir..Irfan kai ne?!"

 

Shi ma a lokacin yake tambayarta "Matata ke ce kika mayar mini da kanki haka?" Yana nuna ta da yatsa.

 

Sai a lokacin ta tuna kalar suturar da ke jikinta, ta sake sunkuyar da kanta, karo na farko kenan da ta ji kunyar wani ya ganta sanye da ɗamammun kaya tun lokacin da bariki ta buɗe mata ido. Don kuwa za ta iya barin gari da wannan shigar ba tare da hakan ya dame ta ba.

 

D.p.o ya kalli Irfan "Ita ɗin ce kenan?"

Ya gyaɗa kai, a take ya ji wani bargon kunya ya lulluɓe shi tare da jin haushin Mahee a karo na farko.

 

A nan dai d.p.o ya ba su belinta saboda alfarmar mahaifin Umar, tare da alƙawarin cewa za su je duba marar lafiyar da ta yi wa sanadin kwanciya da iyayensa.

A nan suka samu information akan asibitin suka fice, ta bi su a baya ƙyalau ƙyalau.

A ranta take ta tunanin lallai Irfan ya cika mai ƙaunarta da gaskiya, ada ba ta so ta sake haɗuwa da shi ba sai bayan cikar burinta, amma a yanzu ba ta da burin da ya fi ta bi bayansa ya maida ta ga ahalinta domin ya zo akan lokaci, a kuma dai-dai lokacin da ta fahimci ba komai a cikin rayuwar bariki sai ƙasƙanci.

Tun lokacin da Umar ya fara jan motar Ba wanda ya yi magana a cikinsu, kowa da abin da yake saƙawa a ransa.

Sai can Umar ya yi ƙarfin halin cewa "Abokina a'ina zamu sauke ta?"

Kafin Irfan ya yi magana ta ce "Ka kai mu gidana, sai mu yi magana a can."

Irfan ya waigo a hanzarce kamar zai yi magana kuma sai ya ɓame bakinsa.

Ta fahimci ƙarin bayani yake nema amma a maimakon ta yi masa bayanin sai ta bige da kwatanta  wa Umar gidanta.

 

 

*******

 

A ɓangaren Sofi rayuwa ta yi mata ƙunci al'amurran gidansu kullum ƙara ta'azzara suke, a ɓangare ɗaya ga tashin hankalin rashin sanin inda masoyinta Irfan ya shige sama da mako ɗaya ba labari. Bayan ta sha da ƙyar a hannun masu bin ta ba shi, shi ne ta zauna ta sake sabon nazari.

Zuciyarta ta bijiro mata da wata sabuwar shawarar da ta yi na'am da ita kai tsaye kuma ta aiwatar da ita, kuma tana saka ran yin nasara a cikin wannan al'amari nan ba da jimawa ba.

 

**********

 

A can Balgori kuwa bayan sun sauka a gidan Maheerah ta shiga ciki ta yi wanka tare da canza suturar jikinta zuwa ta mutunci, ta fito musu da abin motsa baki.

A nan ta warwarewa Irfan zare da abawa akan abin da ya shafi rayuwarta tun lokacin da ta baro gida har zuwa yau. Sannan ta ɗora da cewa "A yanzu na gamsu da ƙaunarka a gare ni ɗari bisa ɗari, kuma a shirye nake na zauna da kai rayuwa ta har abada matuƙar ka amince zaka aure ni. Sai dai fa akwai wani hanzari ba gudu ba."

Ya kalle ta cike da zaƙuwa "mene ne wannan?"

"Sai idan zaka jira ni har zuwa lokacin da zan haihu, na gama bara'a sai mu yi aure. Don kuwa ba zan taɓa iya zubar da cikina ba, iya wadannan zunuban da na kwasa ma sun ishe ni."

Sai da ya zabura jin ta ambaci ciki, amma ya ji a ransa cewa ko duniya ta haife ba zai guje ta ba domin soyayyar gaskiya yake yi mata, yana ƙaunarta ne don Allah kawai ba don wani abu da yake tare da ita ba. Don haka ya ce "Na amince matata ki shirya na maida ki gida jibi sai na nemi aurenki a hannun abbanki domin duk duniya baki da mai aurar da ke sama da shi."

 

Nan take yanayin fuskarta ya sauya ta ce "Ko na yarda zan koma Mambiya ba zan taɓa yarda na koma gidan wannan mutumin da ya cire Ni daga cikin iyalansa ba, don kuwa a yadda na ƙara lalacewar nan nasan ba zai yarda ya karɓe ni ba."

 

A nan yake shaida mata cewa Malam Isah ya yi nadamar abin da ya aikata, a yanzu ba shi da wani buri da fata sama da ya ga dawowarta a gabansa. Ummanta da yayanta ma haka duk da cewa ta shekara biyu zuwa uku ba ta gabansu amma kullum tana cikin ran su.

 

Wannan albishirin nasa ya yi nasarar haƙurƙurtar da zuciyarta har ta amince da batun komawa gidan. Amma ta nemi alfarmar ya ƙara mata sati ɗaya ta kammala shirye-shirye, sa'annan tana so ta siyar da duk abin yake mallakinta ne a garin ta karɓi kuɗaɗenta kafin ta bar garin. Don kuwa idan har ba ziyara ba ba ta fatar dawowa jihar Balgori har abada.

Washe garin ranar suka je duba Ja'afar a asibiti, alhamdulillah jikinsa ya warware sosai. Maheerah ta ƙara ba su haƙuri sa'annan ta yi musu bayanin tuggun da Sorfina ta shirya akan su, a ranar aka sallami Ja'afar, don haka  Maheerah ta koma da su gidanta suka ƙara kwana biyu, bayan sun huta Irfan da Umar suka raka su ta sha tare da biya musu kuɗin mota suka koma Mambiya.

 

Bayan cikar awanni ɗari da sittin da takwas, Maheerah ta gama duk wani shirinta ta haɗa kuɗaɗenta ta zuba a asusunta na banki sannan ta tattare kayanta ta kira Irfan ya zo da motarsa ya ɗauke ta suka hau hanya.

 

Bayan shafe doguwar tafiya sai ga su a garin Mambiya, a nan Mahee ta zama doluwa tana ta kallon yadda aka samu sauyi a garin a yan shekarun da ta yi ba ta nan, wani irin shauƙin son garin ya lulluɓe mata, a take wata nutsuwa ta fara sauko mata da ta ga Irfan ya maida cikin unguwar su.

 

Ƙarfe 6:15 ya faka motarsa a dai-dai inda ya saba tsayar da ita, ba ta jira komai ba ta buɗe motar a hanzarce ta fita daga ita sai hand bag ɗinta tana sanye da wata atamfa dark blue kanta a yane da mayafi mai kalar sararin samaniya wato sky blue.

Ta fara takawa cikin nutsuwa tana nufar lungun gidan su, shi ma ya lashe motar ya biyo ta a baya.

 

Ita ce ta fara saka kai a cikin gidan bakinta ɗauke da sallama yayin da Irfan ya tsaya a soro yana jiran ta masa iso.

 

Umma na zaune kan tabarma tana cin abinci ta jiyo sallamar ta, a hanzarce ta ɗago kanta don ganin mai sallamar, idanunta suka sauka cikin na Maheerah.

 

Ai ba ta san lokacin da ta zabura ta miƙe tsaye tana ƙarewa matashiyar kallo ba, duk da cewa ta ga sauyi sosai a tattare da ita amma hakan ba zai saka ta kasa shaida 'yar da ta kwanta a cikinta wata tara kuma ta yi renonta tsayin shekaru sha tara kafin su rabu ba.

Ganin hakan Maheerah ta zo da gudu ta rungume umma tana kuka, ita ma ummar kukan farinciki take.

 

Sun kwashi mintuna a hakan kafin sallamar malam Isah ta katse musu kukan nasu kusan a tare suka shigo da shi da Sadiƙu da Irfan da suka haɗu a zaure.

Umma ta saki Maheerah ta je ta ɗauko babbar tabarma ta shimfiɗa musu suka zazzauna.

 

Bayan gaishe-gaishe Irfan ya yi musu bayanin inda ya samo ta da yadda aka yi ya yi nasarar dawowa da ita, suka yi masa godiya sosai.

 

Take a wurin Maheerah ta ba wa Abbanta haƙuri akan abubuwan da ta aikata kamar dai yadda ta alƙawarta wa Irfan a hanyar su ta dawowa.

 

Cikin raunanneb sauti malam Isah ya ce "Na yafe miki tuni, da ma ba laifinki ba ne, laifina ne da na kasa ɗaukar ƙaddarar da ta same ni a wancan lokacin, idanuna suka makance daga hango illar da ke cikin korar 'ya mace daga gida, ke ma ki yafe mini 'yata."

 

Cikin kuka ta ce "Ni na fi dacewa da bayar da haƙuri, na manta cewa mai fushi da iyayensa baya taɓa ganin dai-dai a rayuwarsa. Kuma na sake dawo muku da abin kunyar da yafi na baya, matuƙar na haifi cikin nan nasan na jawo muku abin gori na har abada."

 

"Ba ma zan bari hakan ta faru ba in sha Allah, ina komawa gida zan sanar da Alhajina halin da ake ciki, kafin nan zan so duk wanda ya zo taya ku murnar dawowar Maheerah ku sanar da shi cewa ta yi aure a can garin da ta zauna. Daga nan an kashe bakin magulmata tana haihuwa sai a ɗaura mana aure Insha Allah." Irfan ne mai wannan zancen.

 

Malam Isah ya rasa bakin da zai yi wa Irfan godiya kawai sai ya shiga jero masa addu'oin samun nasara da fatar gamawa da duniya lafiya.

 

Sadiƙu ma rasa ya yi inda zai saka Irfan tsabar farincikin da ya yi solar zamowarsa a ciki.

A nan dai Irfan ya yi musu sallama Sadiƙu ya raka shi har mota ya tafi gida cike da walwala.

 

Koda ya ƙarasa gida sashensa ya fara zuwa ya yi wanka ya kimtsa ya ci cake da lemu sannan ya fito zuwa sashen alhajinsa.

A lokacin suna tsaka da cin abincin dare ya sallama cikin falon, cike da murna iyayensa da ɗan'uwansa suka yi masa sannu da zuwa, shi ma ya jone su suka ci abincin.

Bayan kammala ya fuskanci Alhajinsa "Alhaji ina da wata muhimmiyar magana da nake so mu yi."

 

Jin hakan ya saka suka baro dinning zuwa tsakiyar falo suka zauna, a nan ya koro musu bayanin inda ya je da kuma ƙudurinsa na auren Maheerah sai dai ya ɓoye musu zancen sana'ar da ya tarar da ita a kai da kuma cikin da ke jikinta.

 

Alhajinsa ya ja dogon numfashi ya sauke kafin ya ce "Na ji ƙudirinka kuma na lura ka ƙwallafa rai akan wannan yarinyar, don haka ni ba zan hanaka aurenta ba, sai dai kafin nan yana da kyau ka sani akwai wani haƙƙi mai nauyi da muka ɗora akanka ba tare da saninka ba, yana da kyau ka fara sauke wannan haƙƙin kafin ka jajibo zancen aure."

 

Irfan bai san dalili ba ya ji bugun zuciyarsa na ƙaruwa kansa ya yi ɗif, ya ɗago fuskar shi cike da neman ƙarin bayani ya kalli mahaifiyar shi kana ya mayar da dubansa ga Alhajinsa.

 

"Ban fahimta ba Alhaji, ka saka ni a duhu."

Alhajin ya ƙawata fuskarsa da murmushi sannan ya ce "Aure na daura maka ba tare da saninka ba."

"What? Aure fa na ji ka ce?" Irfan ya faɗa yana zato ido tare da dafe kirji.

"Sosai, yau tsayin sati ɗaya kenan da ɗaurin auren, bayan tafiyarka Balgori wani dattijo abin tausayi ya zo har nan gidan ya same ni  yana kuka da magiyar na haɗa aurenka da yarsa da take kwance a asibiti rai a hannun Allah dalilin cutar sonka da take.

  A lokacin na tausaya masa matuƙa ganin yanayin da yake ciki. Na bi shi har asibitin na ga yar tasa, na dawo gida muka zauna da Hajiya muka yi shawara a nan kai ma muka duba yanayin damuwar da kake ciki na rashin waccan yarinyar. Hakan ya saka muka yanke shawarar aurar da ku ko ka samu nutsuwar ruhi ka manta da waccan korarriyar. Ba tare da ɓata lokaci ba na biya sadaki aka ɗaura aurenku da ita, cikin kwana biyu da samun labarin auren naku ta murmure kamar ba ita ke ciwo ba."

"Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un! Abba me ya sa kuka mini haka baku sanar da ni ba?"

 

"Mun yi hakan saboda ceto rayukanku, kuma mun ɓoye maka hakan saboda gudun jefa ka a damuwa yayin da kake wata jihar, mun bari har ka dawo ne sai mu sanar da kai." Alhajinsa ya mayar masa da amsa.

Tsabar damuwar da kalaman mahaifinsa suka jefa shi a ciki bai samu damar yin magana ba sai miƙewa da ya yi ya nufi sashensa.

Alhajin ya sake cewa "Sunan yarinyar Safiya Mudi tana zaune a unguwar Garwa ne sai ka je ka ganta."

 

Sai dai Irfan bai ji ko harafi ɗaya a cikin zancen mahaifin nasa ba, yana ta saƙe-saƙe a zuciyarsa.

'Allah Ya gani ba shi da buri a kan kowacce 'ya mace bayan Mahee taya zai iya haɗa ta da wata macen kuma ya iya kwatanta adalci tsakanin su?'

Haka ya isa sashen shi dafe da kai, kansa yana hautsinawa ya kwanta akan doguwar kujera.

Kwanciyar shi kedawuya kiran Mahee ya shigo wayar, idonsa kur akan screen ɗin wayar har zuwa lokacin da ta tsinke bai yi yunƙurin ɗagawa ba, saboda bai san me zai faɗa mata ba.

 

******

A can gidan su Mahee kuwa kusan kwana suka yi a zaune suna murnar dawowarta gare su, tana ba su labaran abubuwan da suka faru da ita tun bayan fitar ta daga gida.

 

Bayan kwanaki uku Irfan ya haƙura da ƙaddarar aurensa da Sofi, ya nemi kwatancen gidansu ya je don ganin yarinyar da ƙaddara ta haɗa aurensu. Kuma take da haƙƙi akansa fiye da Maheen da yake riritawa.

A nan ya sha mamakin jin cewa unguwar su ɗaya da Maheensa wataƙila ma sun san juna.

Bai gama shan mamaki ba sai a lokacin da mahaifinta ya shiga ciki ya kirawo ta, fitowar ta ke da wuya idanunsa suka faɗa cikin nata, ya yi tsaye turus ya kasa cewa komai.

Sai ita ce ta sakar masa lallausan murmushi ta ce "Ka daina mamaki mijina, ba abin da Allah ba zai iya yi ba, daga kallon farko na faɗa tarkon sonka kai kuma ka faɗa na tsana ta, sai ga shi silar wannan haɗuwar Allah ya ƙadarto aure a tsakaninmu, da ma na faɗa maka cewa kai nawa ne kuma sai na mallake ka duk rintsi."

 

Ya ja wani malalacin tsaki cike da jin haushinta ya ce "Ko ke mayya ce ya ci ace kin rabu da ni, amma tunda kin na ce harda haɗa makircin da aka aura mini ke, zaki shigo gidan nawa sai ki tsinci uwar da zaki tsinta."

Ya ja dogon fasali kafin ya ɗora "Na sani a yanzu kina da haƙƙoƙi a kaina kuma zan yi ƙoƙarin sauke wa, sai dai ina so ki sani, ba zaki samu adalci ba ba wata mace da zan iya kwatanta adalci tsakaninta da abar ƙaunata Maheerah."

 

Yana gama faɗa ya ciro compliment card ɗinsa da bounch na ɗari biyu ya miƙa mata yana faɗar "Karɓi wannan ki riƙe a wajenki, ki yi wasu bukatun wannan kuma katina ne idan kina da wata matsala ki kira ni."

 

Daga haka ya juya, har ya gama surutunsa ya juya ba ta ce komai ba sai murmushi da take a hankali ta furta "Ina daɗa godiya ga Ubangijin talikai da ya mallaka mini wannan tsadadden mijin da na san ya fi ƙarfina ba da tsimi ba bare dabara."

Ta juya zuwa ciki.

 

Bayan kamar sati biyu da dawowar Irfan daga jihar Balgori, amarya Safiya ta tare a ɗakin mijinta, zaman auren su zama ne irin wanda ba a cika samun shi ba.

Amarya Sofi tana iyakacin bakin ƙoƙarinta don ganin ta kyautatawa angon nata da yi masa biyayya. Yayin da shi kuma yake iyakacin ƙoƙarinsa wurin ganin ya sauke hakkokin ta da suka rataya a wuyansa, musamman ɓangaren ci, sha da sutura har ma da inganta lafiyarta ba ya wasa. Sai dai kwata-kwata amaryar ba ta gabansa kuma ba yada lokacin ba ta, gabaki ɗayan lokacinsa ya sadaukar da shi ga aikinsa da kuma kula da Mahee da ɗan cikinta.

Bayan watanni Shida Mahee ta santalo kyakkyawan ɗanta mai kama da ita sak.

 

Irfan ya tsayu kai da fata wurin kula da lafiyarta da ta jinjirin da aika haifa da jinya. Sai dai cikin ikon Allah yaron ko sati bai rufa ba ya mutu.

Mutuwar ɗan ta zowa Irfan da iyayen Mahee ta fuska biyu, ta ɗaya fuskar suna cikin alhini da tausayin Mahee akan wannan rashin, ta ɗaya fuskar kuwa suna godewa buwayi gagara misali da ya ɗauke ɗan da girmansa zai bar ba ya da ƙura.

Da ƙyar Irfan ya haƙura ta yi kwana arba'in na jego, ya matsanta da zancen auren su. A cewarsa ba abin da za a jira da ma ana yin Bara'a ne don tabbatar da samun kuɓutar mahaifa, ita kuwa tata an tabbatar da kuɓutarta tun da ba ta ji ma da haife abin da ke ciki ba.

 

Bayan cikar kwanakin a ranar wata Lahadi da misalin ƙarfe 10 na safe dubunan mutane suka shaida daurin auren Maheerah Isah da Irfan akan sadaki Naira dubu ɗari.

 

Ranar Irfan cike yake da tsananin farinciki mara misaltuwa, a daren ranar aka miƙa amarya zuwa ɗakinta, wanda gida dabam ne da na Sofi ba ma a unguwa ɗaya suke ba.

 

Ita Sofi gidanta Alhaji ne ya siya kuma ya sanya komai a ciki, yayin da gidan Maheerah ya lunka wancan sau biyu a girma kuma Irfan da kan shi ya siya, da ma akwai gidan kuma ya riga ya saka komai a ciki gyarawa kawai aka yi aka saka masa amaryarsa a ciki.

 

A ranar da Sofi ta samu labarin daurin auren ta sha kuka a daren ranar har ta ba wa uku lada, kuma sai a ranar ne ta ji ta yi nadamar auren wanda ba ya ƙaunar ta.

 

A ɓangaren Maheerah kuwa ranar ta yi kukan farinciki kuma ta godewa Allah da ya kuɓutar da ita daga hannun kaɗangarun bariki ya ganar da ita gaskiya ya dawo da ita girbar gaskiya kafin lokacin ya ƙure mata.

 

******

 

Bayan shekara uku komai ya gama dai-daita tsakanin Sofi da Maheerah ƙauna ce tamkar irin wacce take tsakanin yaya da ƙanwarta, da ma can akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin iyayensu mata. Sun haɗa kan su sun riƙe mijin su da amana.

 

Irfan kuwa ganin kyautatawar da Sofi take yi wa Mahee da ƙaunar da take nuna mata sai ta fara shiga zuciyarsa har ya fara kula ta.

 

Da yammacin ranar Litinin Irfan ne sanye cikin wata dakakkiyar shadda ya fito daga ɗakin mahaifinsa ya kalli matansa da suke zaune a ƙasa kusa da mahaifiyarsa suna ta hira cikin raha suna cin wani abu da bai gane ko Miye ba, ya ce "Inyeeah! Matan nan kuna jin dadinku da yawa, wato Hajiya ta shagwaɓa ku da yawa har wani abu ta baku kuke ci ba ta ajiye mini ba."

Suka saka dariya, yayin da hajiyar take ƙoƙarin ɗaga Zainab (yar shekara ɗaya) daga cinyarta tana faɗar "I mana, ni yanzu na daina yayinka ta yan biyuna nake Maheerah da Safiya, karɓi wannan lukutar 'yar taka mai tsinannen nauyi so take ta ɓalla mini cinya to ba zan iya ba."

Ya saka hannu ya karbi yar yana faɗar "Kai Hajiya, hausawa fa sun ce abin cikin ƙwai yafi ƙwai daɗi, ina ga dai kawai kishi kike saboda tafi yarki Maheerah kyau duk da cewa ita ta haife ta."

Su dai su Mahee ban da dariyar dramar ɗa da mahaifiyarsa ba abin da suke.

 

Ya kalle su "Ku tashi mu tafi kun ji matan nan." Suka miƙe Maheerah tana neman zanin goya 'yarta yayin da Sofi ta rarumi jakarta ta miƙe tana tafiya da ƙyar tana turo ciki. Abinka da mai tsohon ciki wata takwas. Bayan Maheerah ta goya 'yarta suka yi wa Hajiya sallama ya shiga gaba matansa na take masa baya suka jera suna hira cikin raha a haka har suka ƙarasa parking space suka shiga motar ya ja suka bar gidan.

 

 

Ƙarshe

 

A nan na kawo karshen wannan littafi Mai suna wata unguwa da fatan zaku yi amfani da fadakarwar da ke ciki ku watsar da munanan ɗabiu da halayen da suka zo a labarin, sa'annan duk kusan komai na cikin labarin ƙirƙira, idan ka ji wani abu da ya yi kama da rayuwarka to arashi ne kawai.

 

Ku tara da ni a littafi na gaba in sha Allah.