Daga Habu Rabeel, Gombe.
Sababbin Likitocin da aka yaye karo na farko a jami’a mallakar jihar Gombe kimanin su 22 sun yi barazanar barin aikin biyo bayan kasa biyan su albashin tsawon watanni biyar da gwamnati ta yi, tun bayan daukar su aiki watan Yulin shekarar nan.
Lokitocin da aka dauka suke koyon aiki a matsayin kananan likitoci masu sanin makamar aiki sun koka matuka na yadda gwamnati ta gaza cika alkawarin fara biyan su kasancewar wasunsu suna da iyalai wasu kuma suna kula da iyaye.
A wani taro manema labarai da suka kira a dakin hutawa na likitoci a asibitin kwararru ta jihar, sun koka matuka kan wannan matsalar ta bakin daya daga cikin su Dakta Kabiru Abdullahi.
Lokitocin sun ce a matsayin su na sababbin likitoci da gwamnatin jihar Gombe ta yi shelan ta dauke su aiki har ta basu gidajen kwana a cikin asibitin, dama wannan yana daga cikin ka’ida kafin su fara aiki sannan aka su a tsarin biyan albashin likitoci sai gashi har yanzu wata biyar ba’a fara biyan su ba.
Ya ce sun bi duk wata hanya da ya kamata gwamnati ta ji su ta saurare su amma har yanzu shiru, kuma a cikin su wasu da dama kamata ya yi ace sun dauke wa iyayensu ko kannensu wata dawainiya amma sai gashi dawainiyar kan su ma ta gagare su da kyar suke iya ciyar da iyalansu.
Dakta Kabiru, ya ce wani lokacin abun da za su ciyar da iyalan su yana gagaran su domin akan wayi gari mutum bai da yadda zai sarrafa gidan sa kuma a haka ake so ya duba marar lafiya gaskiya a cewar su akwai kuskure babba.
A cewar sa su ba su shiga jarida dan su bata gwamnati bane sun shiga dan aji kukan su a saurare su domin yanzu haka wasu daga cikin su sun fara ajiye aikin suna tafiya kuma suma nan gaba kadan suna hanya muddin bata canja zani ba.
Yace yanzu haka mutum uku a cikin su sun tafi kuma wasu ma na biya da su muddin gwamnati ta gaza daukar mataki da zai magance matsalar.
Daga nan sai yace idan aka ci gaba da hakan za’a samu nakasu domin likiti ya duba marar lafiya cikin yunwa da tunani mai makon ya bai wa marar lafiya maganin da ya dace sai kaga an samu akasin haka.
“ Idan Likita yana on call yakan yi aiki ne na tsawon sa’oi 30 a sati guda babu hutu kuma ga ba kudi iyalan ka baka iya kula da su ta yaya za’ayi likiti ya samu nitsuwar da zai duba marar lafiya har ya bashi maganin da ya dace zai yi wuya ” inji shi.
Daga nan sai suka yi kira ga gwamnati da ta duba hanyar magance lamarin domin komai kishin jihar su da suke dashi fa sun rika sun kai ga makura.
Wakilin mu ya kokarin jin ta bakin kwamishinan lafiya na jihar Dokta Habu Dahiru lamarin ya citura.