Wane ne Halilu Sububu, ƙasurgumin ɗanbindigar da sojojin Najeriya suka kashe?
Bayanai da BBC ta samu daga majiyoyinta a jihar Zamfara sun tabbatar da kisan Halilu Buzu wanda aka fi sani da Halilu Sububu wanda shi ne ƙasurgumin ɗanbindigar da jami'an tsaron Najeriyar ke nema ruwa a jallo.
Sojojin dai sun samu nasarar kisan ɗanbindigar ne bayan ɗauki ba ɗaɗi tsakaninsu da wani gungun ƴan bindiga a tsakanin kwanar Dogon Ƙarfe zuwa Mayanci a ƙananan hukumomin Zurmi da Anka.
Ɗanjarida a yankin wanda ya tattaro bayanai kan abin da ya faru, Mannir Fura Girke ya shaida wa BBC yadda al'amarin ya faru.
"Jami'an tsaro sun samu bayanan sirri da ke nuna cewa ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu zai wuce da tawagarsa. Yana tafiya da rakiyar ƴanbindiga fiye da 60 kuma inda tun Magribar yammacin Alhmais har zuwa asubar yau Juma'a.
A nan ne kuma aka wannan ba-ta kashi kuma sojoji suka samu damar kashe shi tare da manyan kwamandojinsa bayan samun nasarar karɓe babura fiye da 20 da alburusai da sauran nau'in makamai." In ji Fura Girke.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da hakan a shafinta na X, inda babban hafsan sojojin Najeriyar, Janaral Christopher Musa yake shaida wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Dare cewa "kwanan Bello Turji da sauran ƴan ta'adda ya ƙare kuma ya kamata kisan Halilu Sububu ya zama izna gare su."
Wani bincike da jaridar PRNigeria ta yi ya nuna cewa Halilu Sububu ne ya kitsa kisan mai sarrafa jirgin nan maras matuƙi na hukumar farin kaya ta DSS kimanin watanni biyu da suka gabata.
Ɗanjarida Mannir Fura Girke wanda ke bibiyar al'amuran ƴan bindiga a yankin jihohin Zamfara da Sokoto ya faɗi abubuwa guda shida a kan shi wannan ɗan bindiga:
- Halilu Buzu ko kuma Halilu Sububu ko kuma Kachalla Halilu Tubali.
- Shi ne madugu ko shugaban ƴanfashin daji da ke arewa maso yamma baki ɗaya da ke kisa da satar jama'a.
- Halilu ya shahara wurin fataucin makamai.
- Ya yi ƙaurin suna wajen haƙar ma'adanai kamar gwal da safararsu zuwa ƙasashen waje.
- A kwanakin baya sojojin Najeriya suka ayyana shi a ɗan ta'addan da suke nema ruwa a jallo.
- Jami'an tsaro sun ce Halilu Sububu ko Buzu ɗan jamhuriyar Nijar ne