Wamakko Ya Ziyarci Katsina Da Kano Domin Gabatar Da Ta'aziya

Wamakko Ya Ziyarci Katsina Da Kano Domin Gabatar Da Ta'aziya
 

 Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto tare da tawagarsa daga Jihar katsina bayan gabatarda gaisuwar rasuwar mahaifiyar sanannen dan kasuwar nan a Katsina Alhaji Dahiru Mangal, sun isa a Jihar Kano wajen Alhaji  Tijjani Kano domin yi Masa gaisuwar rasuwar Dan Uwansa Alhaji Sani Baki Wanda Allah ya yiwa rasuwa kwanan nan.

 

Sanata Wamakko ya yi Kira ga Iyalan Marigayin da su wannan rashin daga Allah madaukakin sarki kana su ci gaba da yiwa Marigayin addu'ar samun rahmar Allah.

 
An gudanar da addu'ar samun rahmar Allah Zuwa ga ruhin Marigayin.
 
Sanata Wamakko a bayanin da mataimaki na musamman kan kafofin sada zumunta gare shi Bashar Abubakar ya ce yana tare da rakiyar Maigirma sakataren zartarwar Asusun amintattu na 'yan sandan Nijeriya Alhaji  Ahmad Aliyu Sokoto da Ubandawakin Gidan Bubu Alhaji  Muhammadu Gidado da tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Sokoto Barista Bello Muhammad Goronyo da sauran su.