Wamakko Ya Yi Kira Ga Magoya Bayan APC Su Fito Don Tarbar Shugaba Buhari

Wamakko Ya Yi Kira Ga Magoya Bayan APC Su Fito Don Tarbar Shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya kawo ziyarar kwana daya a Jihar sakkwato, kan haka jagoran Jam'iyyar APC a Jihar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi Kira ga al'ummar jiha musamman magoya bayan APC da su fito kwansu da kwarkwata domin tarbon shugaban kasa. 
Sanata Wamakko ya bayyana, shugaban kasa zai zo  sakkwato gobe Alhamis domin Buda Wani Gidan siminti Mai zaman kansa da madatsar wutar lantarki Mai karfin mega wat 40 mallakar kamfanin BUA, kana zai yi ta'aziyar rasuwar  bayin Allah da aka hallaka a Wani yanki na sakkwato kwanan baya.
Sanata Wamakko ya sanar da hakan ne  a Gidan sa dake unguwar Gawon Nama  bayan ya dawo Abuja in da yake waƙiltar jama'arsa.
 Wamakko wanda tsohon gwamnan Sakkwato ne ya yi Kira ga magoya baya da su fito  da wuri a tsanake domin wannan tarbon, an san magoya bayan APC da bin doka da son zaman lafiya saboda haka su rike wannan halin da aka san su da shi.
Ya yi fatar Shugaban ƙasa ya zo Sakkwato lafiya ya koma Abuja lafiya.