Wahalar da ake sha a gwamnatin Tinubu Buhari pro-max ne -- Atiku

Wahalar da ake sha a gwamnatin Tinubu Buhari pro-max ne -- Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan har zuwa yanzu gwamnatin APC karkashin jagorancin Bola Tinubu ba ta gane irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki ba, hakan na nufin tun farko ba ta shirya gudanar da mulki ba.

Atiku, wanda ya yi magana ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya bayyana cewa abin takaici ne yadda gwamnatin Tinubu ta bari har sai da yan Najeriya su ka fito kan tituna domin jawo hankalinta kan mawuyacin hali da aka tilasta musu rayuwa a ciki.

Ya ce, “Tabbas akwai kalubale a baya, shi ya sa aka zaɓe ka. Mun san abubuwa da yawa an yi kuskure a lokacin Buhari.

“Tattalin arzikin kasar ya shiga  koma-baya har sau biyu a karkashin gwamnatin APC da ta shude saboda ba ta san komai ba kan tattalin arziki, jajircewa, cin hanci da rashawa ya yi yawa.

“Duk abin da Buhari ya yi ba daidai ba muna ganin na sama da shi a karkashin Tinubu. Abin da muke gani a yau shine Buhari pro-max," in ji shi.