Wa’adin Bello Turji Na kaiwa Talakawa hari: Bafarawa ya jawo hankalin gwamnati
Tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya jawo hankalin gwamnatin tarayya da jihar Zamfara da Sakkwato kan harin ta’adanci da kasurgumin dan bindiga, da ya addabi yankin Sakkwato da Zamfara ya sha alwashi zai kai a farkon watan sabuwar shekara ta 2025.
Tsohon gwamnan a taron manema labarai da ya gudanar a Sakkwato ya ce "yakamata a duba wannan barazanar in dai har dan bandit zai fito ya gayawa kasarsa in ba a biya masa bukatarsa ba lalle ga abin da zai yi, kuma gwamnati tana nan da ranta ta ji abin da ya fada, yakamata ta yi wani shiri na hana aikata kudirinsa.
"Ya ce daga bakin daya ga wata, amma abin bakinciki kafin ranar ya fara akwai wani gari tsakanin Jangeru zuwa Ciki ya tare mutane ya halbe wasu an kone motar, wasu na asibiti a ranar 31 ga wata ya aikata haka.
"Kira na ga gwamnati yakamata ta duba mutane na cikin mawuyacin rayuwa kuma duka hakkinsu na kanta don haka ta fito ta dauki mataki kar ya cigaba da aiwatar da abin da ya fada, shi fa da gwamnati yake fada kuma gwamnati ta zura masa ido talaka na wahala yakamata a gayara,"Kalaman Bafarawa.
Jigo a jam'iyar APC, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi a taron manema labarai a Gusau, ya ce mutane sun shiga cikin fargaba da tashin hankali biyo bayan bidiyon da Bello Turji ya yi inda ya gargadi hukumomi cewa zai kai hari a Shinkafi, Zurmi, a Zamfara da kuma Isa, a Sakkwato idan ba a saki ɗan uwansa, Bala Wurgi, da aka kama ba.
Ya yi wannan barazana ne a ranar Larabar 25 ga watan Disambar 2025 da ta gabata, yana mai cewa lokaci yana ƙurewa kafin ƙarshen shekara.
Dakta Sani Abdullahi ya ce tun bayan fitar bidiyon Turji, fiye da kauyuka 50 a Shinkafi sun zama kufai.
Wannan matsalar hijira ta nuna yadda rashin tsaro ya ƙara muni a yankin, inda al'umma ke kira ga gwamnati ta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
managarciya