Home Uncategorized Uba ya kashe ‘yarsa mai shekaru 20 sabo da ta murɗe masa...

Uba ya kashe ‘yarsa mai shekaru 20 sabo da ta murɗe masa mazakuta

3
0

 

Rundunar ‘yan sanda jihar Akwa Ibom ta kama wani mai suna Sunday Etukudo bisa zargin kashe ‘yarsa mai shekaru 20,  mai suna Ofonmbuk Sunday sabo da hatsaniya da ta tashi a gidan nasa.

 
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Odiko Macdon, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Uyo, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa marigayiyar ta kama masa mazakuta a lokacin da aka samu saɓani, inda ya kuma yi amfani da sanda ya maka mata a kai.
 
Bayan aikata laifin, sai Etukudo ya binne ƴar ta sa a farfajiyar gidansa da ke kauyen Omum Unyiam a karamar hukumar Etim Ekpo a jihar domin ya rufe laifin da ya yi.
 
Daga baya, bayan ya shiga hannu,  ƴan sandan sun tono gawar marigayiyar domin a yi bincike.
 
Sanarwar ta kara da cewa, “Bisa ga sahihan bayanai, a ranar 9 ga Oktoba, 2022, da misalin karfe 1910, wani Ime Sunday Etukudo na kauyen Omum Unyiam a karamar hukumar Etim Ekpo, ya kashe ta ba bisa ƙa’ida ba tare da binne ƴarsa, mai suna Ofonmbuk Ime Sunday, mai shekara 20 a gidansu da ke kauyen Omum Unyiam.
 
“Wanda ake zargin ya yi zargin cewa an samu rashin fahimtar juna a cikin iyali, wanda ya kai ga faɗa, kuma wadda aka kashe din ta rike masa mazakuta shi kuma ya yi amfani da sanda ya buge ta a kai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta, inda kuma ya yanke shawarar binne ta a cikin kabari mara zurfi don ya rufe laifin da ya aikata,”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here