Home Siyasa Tsohon Ministan Sufuri ya fice daga PDP ya shiga ADC a Sokoto

Tsohon Ministan Sufuri ya fice daga PDP ya shiga ADC a Sokoto

9
0

Tsohon Ministan Sufuri a tarayyar Nijeriya Alhaji Yusuf Suleiman ya bayyana ficewarsa daga jam’iyar PDP a wata takarda da ya aikawa shigaban mazabarsa ta Isa ta Arewa a karamar hukaumar Isa a Sakkkwato.

Tsohon ministan wanda ya rike ma’aikatar matasa da wasanni a mulkin shugaban kasa Jonathan ya ce yanke hukuncin ya biyo ne saboda rikicin shugabanci da jam’iyar ke fama da shi da yaki ci yaki canyewa, PDP ta ki samun zaman lafiya.

Ya ce bayan dogon zama dan jam’iyar da ya kasace mai ba da gudunmuwa ga cigaban jam’iyar da kasa baki daya, ya barta ne domin hakan ya zama dole.

Alhaji Yusuf Suleiman ya bayyana komawa jam’iyar ADC domin ba da tasa gudunmuwa ga cigaban kasa da ceto ta daga halin da take ciki na rashin tsaro da tabarbarewar tattalin Arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here