Tsadar Rayuwa: Gwamnan Nasarawa Zai Sayi Abinci Ga Hannu 'Yan Kasuwa

Tsadar Rayuwa: Gwamnan Nasarawa Zai Sayi Abinci Ga Hannu 'Yan Kasuwa
Matsalar tattalin arziki da ke addabar mutane 'yan kasa wanda ya yi sanadin tsadar abinci gwamnatin jihar Nasarawa ta hada kai da kungiyar  'yan kasuwa domin sayo kayan abinci a sayarwa mutane da rahusa. 

Bayan kammala yarjejeniyar gwamnati ta karbi buhun shinkafa 2,100 domin sayarwa mutane cikin sauki.

Gwamna Abdullahi Sule a bayanin da ya fitar ya nuna muhimmancin gwamnatin jiha ta samar da mafita ga abin da zai kara kawo walwala ga mutanen jiha.

"Za mu saye kaya gare su, mu raba Wani kaso na shinkafa kyauta sai mu sayar da sauran da rahusa, haka kuma za mu saye gero da masara a rabawa mutane. Muna kira ga mutane su yi hakuri.

"A daina boye abinci yunwa na addabar mutane, in an cigaba da boye abinci mutane za su cigaba da mutuwa, kar mu mance za mu tsaya gaban Allah" a cewarsa.

Lokacin nan ba a samu ciniki saboda babu ciniki, bai kamata ba mutum ya saye buhun shuga dubu 32 zuwa Wani lokaci ya rika sayar da shi dubu 72,000.