Tinubu Zai Nada Mutanen Da Ba 'Yan APC Ba A Gwamnatinsa

Tinubu Zai Nada Mutanen Da Ba 'Yan APC Ba A Gwamnatinsa

Tsohon ɗan takarar da ya nemi tikitin shugaban kasa a inuwar APC, Nicolas Felix, ranar Talata, ya ce shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, zai ba da mamaki. 

Felix ya ce Tinubu zai naɗa zakakuran mutane masu hazaƙa a gwamnatinsa bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda Punch ta rahoto. 
Jigon APC mai mulki ya yi wannan furucin ne yayin hira da Arise TV ranar Talata 4 ga watan Afrilu. 
Tinubu zai duba kwarewa da cancanta a naɗe-naɗensa ba ruwansa da jam'iyya, inji shi. 
Ya bayyana cewa kowane ɗan Najeriya yana da haƙƙi ba tare da la'akari da jam'iyar siyasar da ya hito ba. 
Ya kara da cewa idan baku manta ba Tinubu ya ce zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa. 
"Asiwaju mutum ne mai saka alheri, mai saka aiki tuƙuru, akwai 'yan Najeriya waɗanda ba mambobin APC masu basira, gogewa da cancanta. 
Na san zai duba har wajen APC ya zakulo mutane." "Amma ina da yaƙinin zai buɗe hannunsu ya ce 'ina son kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, idan kana PDP, Labour Party ko sauran jam'iyyu, mu duka yan Najeriya ne." Jigon siyasan ya roki 'yan Najeriya da su haɗa hannu da Bola Tinubu domin dawo da Najeriya kan turba.