Home Labarai Tinubu ya shirya janye tallafin wutar lantarki daga 2027

Tinubu ya shirya janye tallafin wutar lantarki daga 2027

12
0

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta Tarayya Za Ta Kawo ƙarshen Tallafin Wutar Lantarki da take biya, Ana zargin zai ƙara tsadar rayuwa

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta daina biyan tallafin ɓangaren wutar lantarki daga shekarar 2027.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a.

A cewarsa, matakin na daga cikin shirin gwamnatin na sake fasalin bangaren wutar lantarki domin ya kasance mai dorewa ba tare da dogaro da tallafin gwamnati ba.

Masana na ganin cewa idan aka aiwatar da wannan tsari, akwai yiwuwar farashin wutar lantarki ya ƙaru, musamman idan ba a samar da wasu hanyoyin rage tasirin sauyin ba. Hakan kuma na iya janyo hauhawar farashin wasu kayayyaki da ayyuka, domin masana’antu da ‘yan kasuwa da dama na dogaro da wutar lantarki wajen gudanar da harkokinsu, kuma karin kuɗin samar da kayayyaki kan iya shafar farashin da masu amfani ke biya.

Sai dai ministan bai bayyana cikakken tsarin yadda za a aiwatar da wannan sauyi ba, ko irin matakan da gwamnati za ta ɗauka domin rage tasirin hakan ga ‘yan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here