Taron Makon Danfodiyo: Wane Yafi Dacewa Gwamnan Sakkwato Ya Yi Wakilci Ko Halarta?

Shekara ba ta gadon shekara a taron wannan shekara Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto bai samu halarta wurin taron ba da kansa, sai dai ya tura wakili a wurin taron

Taron Makon Danfodiyo: Wane Yafi Dacewa Gwamnan Sakkwato Ya Yi Wakilci Ko Halarta?

 

Majalisar Sarkin Musulmi tare da wasu kungiyoyin addini a jihar Sakkwato sukan shirya taro kan aiyukkan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo duk shekara wanda wannan ne karo na 10 da aka yi.

A ranar karshe ta taron takan fado dai-dai da ranar da Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya hau karagar Sarautar gidan Danfodiyo in da ya gadi kakansa, kan haka sai a gabatar da Kasida daga bakin wani babban Malami da ya shahara a kuma bayar da kyaututtuka ga wasu mutane da aka yaba kwazonsu da nufin zaburar da mutane masu tasowa, da kuma kara ilmantar da jama'a aiyukkan Shehu Ussman Danfodiyo.

A wurin taron akan samu halartar manyan mutane masu mulki da dukiya a cikin jihar Sakkwato da wajenta don sanyawa ranar albarka.

Shekara ba ta gadon shekara a taron wannan shekara Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto bai samu halarta wurin taron ba da kansa, sai dai ya tura wakili a wurin taron.

Managarciya ta fahimci rashin halartar Gwamnan ya haifar da cece-ku-ce a cikin birnin Sakkwato in da mutanen da dama ke ta fadin albarkacin bakinsu ra'ayoyi da dama sun bambanta kan lamarin. 

Wasu gefen mutane na ganin ba dole ba ne sai gwamna ya halarci taron matukar yana da wani uzuri babba da ya shafi cigaban jiha, domin zamansa a wurin cilas ne ba ganin yana da wakillai da za su yi komai matukar baya nan, "rashin ganin gwamna a zahiri ba wani abin ya madidi ne ba tun da akwai wakilinsa, kuma kowa yasan da ganin ba a ga gwamna a wurin irin wannan taron ba, dole akwai babban uzuri da ba sai an yi magana a kai ba."

A wani gefen kuma mutane na ganin rashin dacewar hakan, yakamata gwamna ya je da kansa a wurin, ba tare da tura wakilci ba, ganin irin bakin da aka gayyato kuma shi ne mai masaukin baki, "muna ganin duk uzurin gwamna kamata ya yi, ya ba da lokacin a yi taron tare da shi, abu ne dake da muhimmanci don shi ne shugaban jiha duk abin da za a yi in babu sanya albarkarsa da kansa abin ya ragu sosai matuka, kan haka ba mu ga dacewar wakilci ba."