Tambuwal da Saraki sun ba da gudunmuwar Miliyan 10 ga bukin ranar haihuwar tsohon Sarkin Kano
Tambuwal da Saraki sun ba da gudunmuwar Miliyan 10 ga bukin ranar haihuwar tsohon Sarkin Kano
Gwaman Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki sun bayar da gudunmuwar miliyan 10 ga bukin ranar haihuwar tsohon Sarkin Kano Muhammas Sanusi na biyu.
A bukin na farko da aka gudanar a Kaduna kowanensu ya ba da gudunmuwar miliyan 5 kamar yadda wakilin Saraki Honarabul Ali Ahmad ya sanar ga bukin cika shekara 60 na Khalifan darikar Tijjaniyya a Nijeriya.
A jawabin fatan alheri Gwamnan Tambuwal ya fahimci cewa shekara 60 da mai martaba Khalifa Sanusi na biyu ya yi a rayuwarsa na cike da nauye-nauye da kalubale duk da hakan ba su hana shi kai ga gaci ba yanda yakamata kan haka ya dace ya yi murna “Muna godewa Allah da ya baka yawancin rai kuma muna rokonsa ya cigaba da kare ka a sauran rayuwarka.” A cewar Tambuwal
Ya ce mutum ne jajirtacce dake fadin abin da ke zuciyarsa ba tare da jin shakkun komai ba.
managarciya