Tambuwal  da Jiga-Jigan 'Yan Siyasa 8 Da Suka Tafka Asara  a Zaben Bana

Tambuwal  da Jiga-Jigan 'Yan Siyasa 8 Da Suka Tafka Asara  a Zaben Bana

Jaridar Daily Trust ta jero ‘yan siyasar da ake gani sun yi asara biyu da biyu  a zaben nan, kamar: 

1. Yakubu Dogara Rt. Hon. Yakubu Dogara ya fita daga APC, ya marawa Atiku Abubakar baya a zaben shugaban kasa a karshe kuma jam’iyyar da ya bari ta doke ‘dan takaransa. 
A zaben Gwamnan Bauchi, Yakubu Dogara ya rabu da Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyarsa, ya goyi bayan APC, a nan ma ya burma masu da kafar hagu. 
2. Okezie Ikpeazu Okezie Ikpeazu ya yi yunkurin zama Sanata a 2023, amma jam’iyyar LP ta tika shi da kasa. Bayan makonni LP ta sake doke ‘dan takarasa a zaben Gwamnan Abia. 
Mai girma Okezie Ikpeazu ya na cikin ‘Yan G5 da suka yi fada da Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP. 
3. Samuel Ortom A zaben wannan karo, Gwamna Samuel Ortom ya tashi babu tsuntsu babu tarko domin Peter Obi da yake tare da shi bai yi nasara a zaben sabon shugaban kasa ba. Haka zalika Mai girma Samuel Ortom ya kunyata a zaben Sanatan Arewa maso Yammacin Benuwai, a karshe APC ta doke wanda PDP ta tsaida takara a jiha.
4. Ifeanyi Ugwuanyi Ifeanyi Ugwuanyi yana tare da Gwamnonin Abia da Benuwai a nan, Okechukwu Ezea na LP ya doke shi a zaben Sanata, amma a karshe Peter Mba zai gaji kujerarsa. 
5. Bukola Saraki Da farko Dr. Bukola Saraki ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a PDP amma bai yi nasara ba, a babban zabe kuma ‘dan takararsa, Atiku Abubakar ya sha kashi.
A zaben Gwamna da majalisu, jam’iyyar APC ta koyawa tsohon Gwamnan da PDP hankali a Kwara. Kusan Saraki bai tashi da komai a 2023 ba, kamar dai a 2019. 
6. Sule Lamido Wani jigo a PDP da zai so ya manta abin da ya faru a zaben nan shi ne Sule Lamido wanda bai iya ba Atiku Abubakar da jam’iyyarsa nasara a zaben shugaban kasa ba. A zaben Gwamna a jihar Jigawa, tsohon Ministan yana kallo ‘dan takaran jamiyyar APC ya doke Mustafa Sule Lamido, sannan PDP ba ta samu kujerun majalisa ba. 
7. Aminu Tambuwal Aminu Tambuwal ya taimakawa Atiku Abubakar wajen samun tikitin PDP, amma babu yadda ya iya yayin da Bola Tinubu ya zama zababben shugaban kasa. 
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya rasa jihar Sokoto domin Ahmed Aliyu ya doke ‘dan takarsa, Saidu Ubandoma. Sannan batun zamansa Sanata a 2023 ya na lilo.
8. Simon Lalong A matsayinsa na Darektan yakin neman zaben Bola Tinubu, APC ba ta lashe zaben shugaban kasa a jihar Filato ba, duk da Simon Lalong yana kan kujerar Gwamna. Haka zalika a zaben sabon Gwamna, Jam’iyyar PDP ta doke Dr. Nentawe Yiltwada. 
9. Ibrahim Shekarau Jam'iyyar NNPP ta ba Malam Ibrahim Shekarau tikitin Sanata, amma ya watsar, ya koma PDP.  A karshe Atiku Abubakar bai yi nasara ba, NNPP kuma ta ci zabe.