Tallafin Bashi Ga Manoman Auduga Na Nijeriya Ya Habaka Noma A Arewa-----Sadik Ado

Tallafin Bashi Ga Manoman Auduga Na Nijeriya Ya Habaka Noma A Arewa-----Sadik Ado
 
Daga Habu Rabeel Gombe.
 
Alhaji Sadiq Ado, mataimakin shugaban kungiyar masu noma da kasuwancin auduga na Najeriya 'Cotton Producers and Merchant Association of Nigeria (COPMAN)' shi ne ya bayyana cewa bashin noma da babban bankin Najeriya CBN ya bai wa manoman auduga na shirin nan na anchor borrowers ya habaka tattalin arziki da noman audugan a yankin arewa.
 
Sadiq Ado, wanda har ila yau shi ne shugaban kungiyar na shiyar arewa maso gabas, yace da a baya noman audugan yana gagara domin da yawa manoma basa iya yin noman amma da zuwan shirn anchor borrowers nan da nan harkar ta bunkasa kuma noman ya yi daraja.
 
Yace sai dai matsalar da suke fuskanta shi ne wasu manoman basu yarda bashi aka basu ba domin basa dawo wa da kudin wasu kuma dakyar suke iya dawo da kashi 10 cikin dari.
 
Ya kuma ce matsalar makiyaya shi ne su Fulanin suna da wani camfi a ran su da auduga wanda suna ganin idan shanun su suka ci auduga zai kara musu Nono da Nama shi yasa suke cinye audugar su tsaya basa gudu idan aka musu magana su ce za su biya.
 
A cewar sa kamar a jihar Gombe gwamnatin da hadin guiwar ma’aikatar aikin Gona sun taimaka wa harkar noman auduga  wanda hakan yasa manoma sun zabura sun samu kwarin guiwa yin noman.
 
Sadiq Ado, ya kara da cewa shigowar da gwamnati tayi a harkar Noma yasa yanzu ana samun manoma suna iya dawo da kashi 50 cikin dari wasu kuma suna dawo da kashi 100 domin sun tsaya da kafar su.
 
Yace irin audugar da ake shukawa a Gombe a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ne aka kirkire shi wata shekara wanda kuma irin yana da kyau idan aka noma audugar tana da zare mai tsayi.
 
Sannan a shekarun baya can lokacin akwai sashin kula da hada-hadar auduga ba’a samun algus ana sayar da auduga akan farashin bai daya babu wani banbanci amma yanzu algus ya yi yawa ana ha’inci shi yasa farashi ya banbanta.
 
Kuma farashin da auduga tayi shi ne yake karawa manoman kwarin guiwa saboda zaka noma a bika har gida a saya amma rashin farashin shi yake kashe musu guiwa
 
A cewar sa kuma yankin Borno da Yobe an samu koma baya sanadiyar tashe-tashen hankali na Boko haram wanda ba iya noman auduga kadai ne ya koma baya ba komai ma a yankin an samu cikas amma da ba dan haka ba da suma suna noma auduga sosai, sai dai a bangaren kudanci irin garuruwan Biu da Kwaya kusar da Hawul yanzu haka suna  dan taba noman a lokacin da hankali ya fara kwanciya.
 
Yace farfado da noman audugar yasa aka farfado da kamfanonin gurzar ta a yankin wanda yan kasuwa kan yi hada hadar su kai tsaye da kamfanonin suna gurza musu suna kuma saya daga wajen su.
 
Alhaji Sadiq Ado, ya yi amfani da wannan damar ya yi kira ga manoma da cewa su taimaka suna dawo wa da wannan rance da aka basu saboda wasu ma su amfana domin rashin dawo da wannan bashi zai haifar da koma baya sosai.
 
 Hoto Alhaji Sadiq Ado