Talban Gombe ya hidimtawa Maulidi da Masu yinsa a Gombe--- Sharu Auwal Siddi
Daga Habu Rabeel, Gombe.
Shugaban kungiyar Mawakan Manzon Allah SAW na Ushaqun Nabiyi Rasulil A,azam Sharu Auwal Siddi Bolari, Talban Sharifan Najeriya yace Talban Gombe kuma tsohon gwamnan na Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, har yanzu ba'a samu kamar sa ba a shugabanin da akayi a jihar wajen yiwa Manzon Allah hidima musamman a lokutan Maulidi na Fiyayyen halita da kuma na Shiek Ahmadu Tijjani.
Sharu Auwal Siddi Bolari wanda shi ne Talban Sharifan Najeriya, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu kan shirye-shiryen Maulidin sheik AhamaduTijjani Abul Abbas, da aka shirya za'a gudanar a ranar 24 ga watan nan na Satumba a Gombe
Yace Tsohon Gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo, shugaba ne da a lokacin mulkin sa ya dauki dawainiya na taimakawa yan Darika zuwa kasar Senegal dan halartar Maulidin shiek Ahmadu Tijjani, har ya gama mulki sa kuma yana taimakawa harkar Maulidi inda dul lokacin Maulidi yakan bi tsangayoyi yana basu tallafin kudi da na abinci.
Ya kara da cewa yanzu haka ana kan shirye-shiryen Maulidin shiek Ahmadu Tijjani, amma har yanzu babu wani tallafi da suka samu ganin cewa nauyin na wuyan su ne musamman ma yan kungiyar Ushaqun Nabiyi da sune masu masaukin baki.
Talban Sharifan ya jan hankalin mambobin su na Ushaqun Nabiyi da cewa su zama masu da'a kar a dinga samun su a cikin harkokin da basu dace ba domin suna da kima da daraja kasancewar su mawakan fiyayyen Halitta Annabi rahama.
Daga karshe sai ya yi kira ga al'umma musamman masoya manzon Allah da su taimaka wajen ganin an gudanar da maulidin cikin nasara.
managarciya