Taba sigari na hallaka 'yan Najeriya 29,000 duk shekara — Bincike

Taba sigari na hallaka 'yan Najeriya 29,000 duk shekara — Bincike

Hukumar Lafiya ta Duniya ce ta ware duk ranar 31 ga watan Mayun kowace shekara domin gangamin wayar da kan al'umma illolin taba sigari domin kauce wa haɗarinta.

Wani mai bincike kan ci gaban tattalin arziki a Afirka ya ce taba sigari na sanadin rayukan 'yan Najeriya 29,000 a kowacce shekara.

Austin Iraoya da ke aiki da cibiyar tattalin arziki ta Afirka ya ce 'yan Najeriya na kashe naira biliyan 526 wajen shan sigari da neman maganin cututuka da taba ke haifarwa.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito, Mista Austin na cewa wannan al'amari na yin mumunan illa ga tattalin arzikin kasa.

Kuma a cewarsa gwamnati na samun harajin kashi 10 cikin 100 ne kacal, na wadannan kuɗaɗe da ake ɓarnatarwa wajen shan sigari.

Waɗannan bayanai nasa na zuwa ne a lokacin bikin ranar yaƙi da shan taba sigari da aka gudanar a birnin Tarayyar Najeriya wato Abuja.