Ta Kone Kishiyarta Da Ruwan Zafi Saboda Fadan Yara

Ta Kone Kishiyarta Da Ruwan Zafi Saboda Fadan Yara

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau

 

A yaune wata mata yar asalin jihar Zamfara mai suna Luba dake aure a Birnin Tarayya Abuja ta kawo korafin ta, ga hukumar kare hakkin dan adam dake garin Gusau, dan gane da irin ruwan zafin da kishiyar ta ta zuba mata ga jiki wanda yayi sanadiyar jin mummunar rauni, inda tace tana son  a kwato mata hakkin ta.

 
Da take yiwa manema labarai bayani a ofishin hukumar kare hakkin dan adam, dake garin Gusau, malama Luba tace,  fadan su ya samo asaline lokacin da diyar ta  ta  ciji diyar abokiyar zaman ta, ita kuma abokiyar zaman nata mai suna Inna ta sa babbar yarta ta buge wannan karaman yarinyar, daga nan ne suka fara cacar baka har suka kai da bugun juna wanda daga bisani aka rabasu.
 
Ata bakin ta, bayan sun kare sai taga kishiyar tata ta aza ruwan zafi, wanda ita bata tunanin tana da niyyar yi mata wanka da suba.
 
"Ina zaune cikin Daki sai ta kirani da cewa inzo muci abinci kamar yanda muka saba, bayan na fito mun fara cin bincin sai kawai ta tashi kamar zatayi wata lalura, naga ta dauki tukunya ashe ruwan da ta tafasa suna ciki, sai ta biyo ta bayana ta zuba man su.
 
"Daga nan sai nayi kuwa domin insamu ceto, ina cikin wannan yanayi sai kuma ta bini da icce tana duka, saida wasu maza biyu suka ceceni a gunta. Haka taci gaba da cewa wai mu kado bamusan kunya ba kara ta kasheni a huta.
 
"A lokacin ne aka kira mijin mu, yazo yaga halin da nake ciki, bai kaini wajen magani ba a wannan lokaci, saida safe kuma, ina cikin wannan halin ta kara shiga Daki na ta buga man icce ga goshi jini ya kama zuba.
 
"Ganin haka ya sa mijin mu yace kowace taje gidan su, bayan na fito gidan sai ya biyo ni ta baya ya kaini Assibiti, aka yi man magani, sannan muka hau achaba ya kawo ni zuba, ya bani naira dubu ukku wai idan naje gida inbidi magani, amma fa bai bani kudin mota ba.
 
"Ta haka dai nayi amfani da abunda ke garan na shigo Gusau, yanzu uwaye na ke dauke da nauyin magani na, amma ya kira babban yayan mu ya fada masa cewa idan ya samu lokaci zaizo ya duba ni.

 
Da aka tambayeta mi take son wannan hukumar tayi mata, sai tace tanason a bi mata hakkin ta, a biya diyya ga irin barnan da abokiyar zaman ta tayi mata.
 
"Saboda kaga yanzu Idona daya ya lalace, baya na duk da kirjina duk sun kone, ba yadda zanyi in koma kamar yanda nake a lokacin da ya aure ni.
 
A nashi jawabi shugaban kungiyar kare hakkin dan adam na wannan jihar comrade Salisu Umar yace, yanzu haka sun shirya tsab domin zuwa Ofishin su dake Abuja domin kai wannan korafin domin a kama mai laifin da kuma mijin nasu, kuma sai sunbi mata hakkin ta.