Sulhu da 'yan bindiga Masana sun jawo hankalin gwamnatin Sakkwato 

Sulhu da 'yan bindiga Masana sun jawo hankalin gwamnatin Sakkwato 

Masana harkar tsaro da sanin dokoki sun tofa albarkacin bakinsu kan shirin da gwamnatin Sakkwato karkashin Gwamna Ahmad Aliyu take son yi na yin sulhu da 'yan bindiga ga masu bukata a cikinsu.
Babban lauya Barista Sidi Bello ya nuna jin  dadinsa da fatar wannan hakar ta cimma ruwa "dalilai da dama ke sa mutum ya so a samu zaman lafiya, na yi zama ƙananan hukumomin Goronyo da Wurno da Sabon Birni da Isa da Balle ta karamar hukumar Gudu waɗannan wurare su ne suka fi haduwa da matsalar tsaro a yankin Sakkwato nasan wahalar da ake sha kan matsalar, duk abin da zai samar da zaman lafiya a jiha abin bukata ne, jihar Sakkwato mutanenta musulmai ne a mahangar addini ya yarda shugabanni su samar da kafar sulhu da daidaito a cikin wadanda suka samu kansu cikin rashin zaman lafiya, duk laifin da aka yi maka ana iya yafe shi a tsarin addini kar ka yi tunanin wannan ya kone mana rumbun gero ko ya yi garkuwa da dan uwana ya karbi kudi kan haka ba a yafewa."

Dakta Kabiru Jabo masani harkar tsaro ya kalli lamarin  ya ce "duk sanda akwai fitina a tsakanin mutane biyu  sulhu ne karshenta, wannan ba wani sabon abu ba ne domin komai dadewa sai an bi wannan hanyar ta sulhu ko yakin duniya na farko dana biyu sai da aka zauna sulhu, a Ruwanda ma da aka kashe sama da mutum 800 'yan Tuse, a kasar Afirka ta Kudu,  a Siraliyo da Liberiya da Muzambike duk yake yaken da suka yi sulhu aka yi.
"Abin da ake son sani yanda za a yi sulhun don ana son in an yi ya tabbata, dole sai an tsabtace sulhun gwamnati ta yadda za ta yi sulhu da gaskiya, sannan a san wadanda za a nemo su shiga cikin sulhun, domin masana kan tsarin su ake sanyawa, kuma a cikin sulhun sai tare da wakillan mutanen da ake gallazawa na gaskiya ba za a sanya siyasa ba, a gefen 'yan bindiga sai an samu suma da gaske suke yi, in ba a bi wannan tsarin ba, za a yi sulhun  ya zama nawuccin gadi ne ."
Ya ce akwai bukatar gwamnati ta sanya kwararru su yi bincike kan dalilin da ya kawo sulhun Zamfara da Katsina ya lalace bayan an yi don sanin in da za ka fito ga lamarin.
Dakta Shamsu Bello ya ce sulhu abu ne da yake da wuri a addini.
"Abin da yakama gwamnati ta yi shiri kafin sanar da cewa za a yi sulhun, sai dai abin da muke tambaya shin ita gwamnati ce za ta yi sulhu ko tsakani ne za ta shiga, shin gwamnati ake fada da ita ko matsala ce da ta shafi al'umma.
"Duk in da ka ga za a yi sulhu sabani ne tsakanin al'umma biyu, kenan gwamnati tsakani za ta shiga, shin su waye 'yan bindigar nan, a ina suke da zama, su wa suka ja daga, an san 'yan bindigar don kowane nada tasa daba, kan haka dabar su waye za mu yi sulhu da ita, sannan in za a yi da wace al'umma ce za a sulhun ta su. Ba magana ce ta sulhu tsakanin gwamnatin Sakkwato da 'yan bindiga ba, 'yan bindiga ne da al'umma, sai ta hade kansu wuri daya a fahimci laifin kowa.
"Sulhu nada hanyoyi da ake yinsa, ba a sulhu a boye yakamata a yi kowa na biye kan lamarin da ake ciki, a yi sulhu ba tare da sharadi na kudi ba, kar a ce ka je a baka kaza, in an yi haka bai tsaftacce ba." a cewar Dakta Shamsu.