Kwamishinan Makamashi da albarkatun Man fetur na jihar Sakkwato Honarabul Sanusi Danfulani ya shirya zai karbar gayyatar da majalisar dokokin jiha ta yi masa, in da kwamitin majalisa na kimiya da fasaha ya nemi ya bayyana a Talata mai zuwa.
A satin da ya gabata ne Majalisar dokokin ta gayyaci Kwamishinan ya bayyana gaban kwamitin a ranar 5 ga watan Agusta biyo bayan kin girmama ziyarar gani da ido da suka kai a ma'aikatarsa.
Kwamishina Danfulani ya musanta zargin da suka yi masa na ya walakanta 'yan majalisar a lokacin da suka kai rangadi a ma'aikatar makamashi.
Ya ce yana girmama majalisa da mambobinta kwarai da gaske musamman shi tun a farko a majalisa ya fara aiki.
Kwamishina ya bayyana abin da aka samu rashin fahimta ne ya faru a tsakanin mambobin zartarwa dana dokokin gwamnatin jiha.
"Rashin ganina da ba su yi ba ya faru ne kan halartar zaman majalisar zartarwa ta jiha dana yi wanda gwamna ke jagoranta ni mamba ne."
Danfulani ya ce bayyanarsa a gaban kwamitin zai ba shi damar ya yi masu bayanin cigaban da aka samu a wurin aikin samar da wutar lantarki mallakar jiha waton IPP.
A cewarsa aikin ya kai kashi 80 na kammalawa, an sanya watan Okotoba za a soma gwajin wutar.
Ya fahimci cigaban kiyon lafiya da samar da wadatattun ruwan sha da ilmi ya dogara ne kan samar da wutar lantarki.
Kwamishina ya yi kira ga 'yan majalisar da su mayar da hankali wurin karfafa cigaba a wuraren da suka shafi al'umma kamar kiyon lafiya da ilmi da noma da samar da ruwan sha.
Ziyarar da 'yan majalisa suka kai an yi ta ne kan duba aikin samar da wutar lantarki da ake yi karkashin ma'aikatar, jan kafar da ake yi kan aikin yana shan shuka a tsakanin mutanen jiha musamman kudaden da ya lakume ba a kammala ba.
Aikin an fara shi ne tun farkon wa'adin farko na tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya kammala wa,adin mulkinsa ba a kare ba.
Haka Sanata Aminu Waziri Tambuwal shi ma aka yi ta zuba kudi a aikin ya tafi ba a kare ba, sai wannan gwamnatin ta Dakta Ahmad Aliyu a yanzu ta shafe shekara biyu tana zubawa aikin kudi a yanzu aikin sun ce ya kai kashi 80, na kammalawa.