Sokoto da wasu jihohi 15 sun maka EFCC kara a Kotun Koli

Sokoto da wasu jihohi 15 sun maka EFCC kara a Kotun Koli

 
Kotun kolin Nijeriya ta sanya ranar 22 ga watan Okotoban 2024 za ta saurari karar da jihohi 16 suka sanya a gabanta kan kalubalantar dokar da ta samar da hukumar EFCC da wasu biyu.
Alkalan mutun bakwai karkashin jagorancin Uwani Abba-Aji ta sanya ranar Talata domin jin bahasin, bayan da ta bayar da dama ga gwamnotocin jihohi su shiga shari'ar wadda tun a farko gwamnatin jihar Kogi ta shigar da ita ta hannun kwamishinan shari'arta.
Jihohin da suka shiga shari'ar sun hada da Ondo, Edo, Oyo, Ogun, Nasarawa, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Enugu, Benue, Anambra, Plateu, Cross-River da Niger.
Haka ma jihohin 16 suna kalubalantar dokar ta samar da hukumar samar da bayanan sirri ta kudaden kasa(NFIU).
A cewarsu ba a cika ka'idojin doka ba a  wajen samar da hukumomin.