Sojojin Nijeriya da ke samar da tsaro a tawagar Fansar Yamma sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga biyu sun ƙwato makamai da babura a artabun da aka yi da ɓatagarin cikin ƙaramar hukumar Raɓah a Sakkwato.
Farmakin ya faru ne bayan bayanan sirri ingatattu da sojoji suka samu da safen Juma’a ‘yan bindigar sun zo da yawa sun saci shanu a yankin Maikujera, nan jami’an tsaro suka yi yinƙurin hana samun nasara a wurin ‘yan bindigar.





