Sojoji Sun Yi Kofar Rago ga Bello Turji, Ana Kokarin Cafke Shi 

Sojoji Sun Yi Kofar Rago ga Bello Turji, Ana Kokarin Cafke Shi 

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sha alwashin kama babban dan ta'adda, Bello Turji, da ya shahara da ta'addanci a Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Janar Musa ya ce kama Turji abu ne da lokaci kawai ya rage, domin sojoji na ci gaba da gudanar da tsare-tsare wajen ganin hakan.
Da yake magana a wani shiri na musamman da aka watsa a tashar Channels Television, Janar Musa ya ce 'yan ta'adda da dama sun mika wuya a Najeriya. 
Babban Hafsan Tsaro, Janar Musa, ya ce an yi nasarar kakkabe dukkan kwamandojin Bello Turji da suka rika taimaka masa wajen gudanar da ta'addanci a Arewa maso Yamma. “Tun da ya fahimci cewa muna bibiyarsa, sai ya fara buya amma muna ci gaba da gudanar da aiki a kansa. Muna kama duk wanda ke kusa da shi, kuma mun kashe kwamandojinsa.” - Janar Christopher Musa Sojoji na gudanar da hare-hare kan duk masu bayar da goyon baya ga Turji a jihohin Sokoto, Zamfara, da Kebbi, domin tabbatar da cewa ya rasa mafaka ko taimako daga kowane bangare.