Sojoji Sun Kwato Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
Sojojin Nijeriya sun yi kwato mutum 6 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sa wa hannu a ranar Litinin, a garin Kaduna.
Kwamishinan ya ce, daga bayanan da ya ke samu daga filin daga, sojojin da ke sintiri, sun bude wuta kan ‘yan bindigan ne a kokarin da su ke yi na kakkabe ‘yan bindigan da su ke boye a dazukan Kagon Kadi da Labi, da kuma bakin Kogin Udawa.
’Yan bindigan sun tsere sakamakon fin karfinsu da sojojion suka yi, a inda su ka bar wasu mutane 6 da su ke garkuwa da su a sansaninsu.
Sanarwar ta ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i ya yi murna tare da jinjina wannan kokari na dakarun sojin.
managarciya