Sojoji sun kori ƴan ta’addan Lakurawa daga Nijeriya – Sanata Aliero
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Adamu Aliero, ya bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ta kora wata kungiyar ‘yan ta’adda da ake kira Lakurawa zuwa Jamhuriyar Nijar.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, Aliero ya ce wannan ci gaban ya faru ne a ranar Talata bayan shiga tsakani daga Ministan Tsaro, Abubakar Badaru; Babban Hafsan Tsaro, da wasu masu ruwa da tsaki.
Aliero ya ce, “Mun bayyana wa Minista a bayyane cewa idan muka yi wasa da ‘yan ta’addan Lakurawa, abin da ya faru a Arewa maso Gabas na iya faruwa a Arewa maso Yamma.
“Yaki ne da za a iya kammalawa cikin kwanaki biyar, kuma idan muka bari abin da ya faru a Arewa maso Gabas ya sake faruwa a Arewa maso Yamma, zai kasance mai muni. Arewa maso Yamma tana da yawan jama’a sosai, kuma tana da arzikin filayen noma, kiwo, da koguna don noman rani, kamun kifi, da sauran abubuwa, don haka dole ne mu kare yankin.”
managarciya