Sojoji sun yi luguden wuta tsakaninsu da wasu 'yan ta'adda a yankin Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja biyo bayan gano maɓoyar su da jami'an suka yi.
Majiyar mu ta Daily Trust ta ce 'yan ta'addan sun ɗauki mutane huɗu da suka fita yin aiki a gona a ranar Alhamis da ta gabata.
Daga bisani 'yan ta'addan sun aiko mutum ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauke domin ya siyo musu man fetur.
Wakilin wata ƙungiyar matasa a yankin Jibril Allawa ya shaidawa majiyarmu cewa bayan da mutanen garin suka samu bayanai daga gurin wanda aka aiko, sai suka sanar da jami'an tsaro wanda su ka kai ɗauki cikin gaggawa.
A yayin farmakin da jami'an tsaron sojin suka kai, mutane da dama da aka sace sun samu nasarar kuɓuta daga hannun masu garkuwar.
“Wasu gungun 'yan ta'adda ne a kan babura suka zo kusa da Allawa inda suka ɗauki wasu mutane huɗu da suke aiki a gona. Sannan suka aiko ɗaya daga cikinsu da kuɗi domin ya siyo musu mai da abin sha.”
Ya ƙara da cewar mutumin da aka aiko ya yi siyayyar ne ya sanar da al'umma halin da ake ciki inda su kuma suka sanar da jami'an tsaro na soji.
Jami'an sun tasa mutumin a gaba, suka yiwa 'yan ta'addan kwanton ɓauna sannan suka buɗe musu wuta.
Majiyar tamu ta ƙara da cewar anga wasu ƙasurguman 'yan ta'adda wato Kachalla Ali da Layee waɗanda suka addabi yankin Zamfara a wannan dajin. Sojoji uku ne suka samu raunuka a yayin musayar wutar da ta faru tsakanin su da 'yan ta'addan.
The Sun ta wallafa cewa aƙalla 'yan ta'adda 30 ne sojojin suka yi nasarar kashewa a farmakin a yayin da wasu suka gudu da raunuka. Haka nan ma sojojin sunyi nasarar kuɓutar da aƙalla mutane 20 daga hannunsu.