Home Labarai Sojoji sun kashe Lakurawa da ƙwato makamai a Sokoto

Sojoji sun kashe Lakurawa da ƙwato makamai a Sokoto

10
0

Sojin ƙasar nan na rundunar Operation Fansar Yamma, sun kashe wasu da ake zargin ’yan ta’addar Lakurawa ne, tare da ƙwato makamai da babura biyar a Dajin Waria, Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sokoto.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar Alhamis, 15 ga Oktoban 2026.

Ya ce, Sojojin Sashe na 2 na rundunar sun gudanar da aikin ne a hanyar ƙauyukan Alela, Bilange da Kandam zuwa Dajin Waria, inda suka yi musayar wuta da waɗanda ake zargin ’yan ta’addan ne, lamarin da ya sa wasu suka tsere cikin dajin.

Rundunar ta bayyana cewa sojojin sun bi waɗanda suka tsere, inda suka halaka wasu daga cikinsu, sannan suka lalata sansanoninsu da gine-ginen da suke amfani da su tare da ƙwato makamai da babura biyar.

Sanarwar ta ce, Sojojin na ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da sintiri a yankin, yayin da rundunar ta buƙaci jama’a su riƙa bayar da sahihan bayanai kan motsin mutanen da ake zargi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here