Home Beauty & Personal Care SIRRIN HAƊA MAI, MAI KYAU NA GYARAN JIKI A LOKACIN SANYI

SIRRIN HAƊA MAI, MAI KYAU NA GYARAN JIKI A LOKACIN SANYI

18
0

Shin kin lura cewa a lokacin sanyi fata tana saurin bushewa, ta yi ƙaiƙayi, ta rasa laushinta, wasu lokutan ma har ta fara yin fatsi-fatsi?

A wannan lokacin, fata tana buƙatar kulawa ta musamman. Amma shin sai kin kashe kuɗi masu yawa wajen sayen man shafawa masu tsada kafin ki kula da kyawun fatarki? A’a!

Ga wata hanya mai sauƙi da za ki iya haɗa man shafawa mai taimakawa wajen kare fatarki daga bushewa da kuma samar mata da laushi, ba tare da kashe kuɗi masu yawa ba.

Abubuwan da za ki tanada:

  1. Man kwakwa.
  2. Man sunflower ko man zaitun.
  3. Man shafawa (Petroleum jelly).

Yadda za ki haɗa shi:

  • Ki samu ƙaramin kwano mai tsafta kii zuba man kwakwa cokali biyu sannan Ki zuba man sunflower cokali ɗaya ki zuba ƙaramin cokali na petroleum jelly Ki gauraya su sosai harki tabbatar da sun haɗe gabaɗaya.

Ki samu ƙaramar kwalba wacce kika yarda da tsabtarta ki zuba haɗin mayukanki a ciki.

Yadda ake amfani da shi:

Idan kikayi wanka, musamman da ruwan ɗumi ba mai zafi sosai ba, ki busar da jikinki a hankali, amma ki bar fatarki da ɗan danshi. Sai ki shafa man a jikinki domin taimakawa wajen rage bushewar fata.

Abin lura: Wannan haɗin yana taimakawa wajen rage bushewar fata da samar da laushi;

‘Yan uwa mata, me ya sa za mu bar sanyin hunturu ya hana fatarmu samun kulawar da ta dace, alhali akwai hanyoyi masu sauƙi da araha da za mu iya amfani da su?

Kyawun fata yana farawa ne daga kulawa, tsafta da amfani da kayan da suka dace da fatarki.

#Managarciya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here