Shugabar Mata a Jam’iyar  PDP Ta Koma APC a Sakkwato

Shugabar Mata a Jam’iyar  PDP Ta Koma APC a Sakkwato

Shugabar mata a jam’iyar PDP ta jihar Sakkwato Hajiya Kulu Abdullahi  Rabah wadda aka sani da ‘Yar Sardauna ta bar jam’iyar in da ta koma APC kwana hudu kafin zaben Gwamna da aka shata gudanarwa a ranar Assabar a Sakkwato.

Hajiya Kulu Rabah a takarda da ta aikewa shugaban mazabarta a garin Mai Kujera a karamar hukumar Rabah ta sanar da shi barin jam’iyar saboda rashin fahimtar da ke cikin PDP wadda ta hana ciyar da jihar Sakkwato gaba.

Kulu Rabah jim kadan da barin PDP ta bayyana shiga  APC a gaban  jagoran jam’iyar APC a jiha Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da dan takarar Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto.