Shugaban ƙaramar hukumar Tangaza Honarabul Isa Salihu Kalenjeni ya ajiye muƙamin shugaban ya kuma bar jam’iyyar APC Mai mulki a jihar Sakkwato.
Shugaban a wani bidiyo da ya wallafa a kafar Facebook ya ce “sunana Isah Salihu Bashar Kalanjeni zaɓaɓɓen ciyaman na ƙaramar hukumar Tangaza a Sakkwato ina sanar da jama’a na fice daga jam’iyyar APC kuma a yau Talata 7 ga watan Juli 2026 na aje muƙami na matsayin ciyaman a ƙaramar Hukumar Tangaza, ina neman yafiyar mutanen ƙaramar hukuma na kuren da na aikata wanda na sani da wanda ban sani ba, a ƙarshe ina yi wa mutanen Tangaza da Sakkwato fatan alheri,” kalaman Honarabul Kalanjeni.
Wasu bayanai da ba a tabbatar ba an zargi tsohon ciyaman zai shiga jam’iyyar ADC ne kan haka ya ɗauki matakin.






