Shinkafi ya janye takararsa ta neman shugabancin Jamiyyar APC na kasa

Shinkafi ya janye takararsa ta neman shugabancin Jamiyyar APC na kasa

Daga Hussaini Ibrahim.

Dantakara Shugabancin Jamiyyar APC na kasa ,Alhaji Sani Abdullahi Wanban Shinkafi ya bayyana janyewar daga takarar shugabancin Jamiyyar sabo da biyayya ga Shugaban kasa da Uwar Jamiyyar.

 Shinkafi ya bayyana haka ne a Taron da yayi da manaima labarai a Gusau babban Birnin Jihar Zamfara.

Dan takarar shugaban Jamiyyar,ya kara da cewa,ya ayyana qudirinsa na tsawa takara shugabancin Jamiyyar ne a ranar 17/10/2021.sai Kuma na tabbatar ma Uwar Jamiyyar APC ta kasa , aranar 22/1/2022. kuma yau 21/3/2022 , Ina sheda maku cewa, na janye takarata ta shukubancin Jamiyyar, sabo da ni mai biyayane ga Shugaban kasa da Jamiyyar akan ,sunyanke Shawara wannan mukamin na shugabancin Jamiyyar anbarma Arewa ta tsakiya shugabancin Jamiyyar.dan haka ni nabi wannan hukunci,inji Wanban Shinkafi Sani Abdullahi.

'Wanban Shinkafi ya kuma mika godiyarsa sa ga Kodinoninsa na jahohin kasar nan da gwamnoni da magoya bayana da dai sauransu.

Kuma ya kasa bayyana godiyarsa ga Gwamna Bello Matawale da kuma gwamnan Barno da dai sauran su ,acikin wannan tafiya ta.