Home Daga Marubutanmu SHIN KUN SAN WAƊANNAN ABUBUWAN GAME DA MAZAJENKU KO KUWA SAI AN...

SHIN KUN SAN WAƊANNAN ABUBUWAN GAME DA MAZAJENKU KO KUWA SAI AN SAMU SAƁANI SANNAN KUKE FARA ƘOƘARIN FAHIMTAR JUNA?

31
0

Biyo Managarciya domin jin lamarin••

A matsayinki na mace, shin kin taɓa zama kin yi tunani a kan cewa akwai wasu abubuwa da ya kamata ki sani game da mijinki domin samun kyakkyawar rayuwar aure?

Sau da yawa mata suna shiga rayuwar aure da tunanin cewa soyayya kaɗai ce ginshiƙin zaman aure, alhali kuwa akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata mace ta fahimta game da mijinta domin ta iya mu’amala da shi cikin hikima da fahimta.

Ya kamata mace ta san irin abubuwan da mijinta yake so da waɗanda ba ya so. Ta fahimci halayensa, yanayin fushinsa, abubuwan da suke faranta masa rai da kuma waɗanda suke ɓata masa rai. Domin ba za ki iya fahimtar mutum sosai ba idan ba ki ba wa kanki damar sanin halayensa ba.

••Ki san halin mijinki:

••Ki san abubuwan da yake so

••Ki san burinsa da manufofinsa

••Ki san lokacin da yake cikin damuwa:

••Ki san halin tattalin arzikinsa

••Ki san dangantakarsa da iyalansa

••Ki san yadda yake son a nuna masa soyayya

••Ki san raunin mijinki da ƙarfinsa.

••Ki san haƙƙoƙinsa da haƙƙoƙinki

A ƘARSHE:

Ya ke ƴar uwa mace, sanin mijinki ba yana nufin ki rasa kanki ko ki mayar da rayuwarki gaba ɗaya a hannunsa ba ne. Yana nufin ki koyi fahimtarsa, ki san yadda za ki zauna da shi cikin mutunta juna, tausayi da kulawa.

Kada ki jira sai an samu matsala kafin ki fara ƙoƙarin fahimtar mijinki. Haka kuma, kada ki manta cewa shi ma yana da alhakin sanin abubuwan da suka shafe ki.

Domin kyakkyawar rayuwar aure ba ta ginuwa da ƙoƙarin mutum ɗaya kawai, tana buƙatar fahimtar juna, haƙuri, amana, sadaukarwa da sauransu.

#managarciya 

#Managrciya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here