Akwai haƙƙoƙi da dama da ya kamata miji da mata su san su, su fahimci cewa haƙƙoƙi ne da Allah Ya ɗora wa kowannensu a kan ɗayan. Domin aure ba wai zama tare a gida ɗaya kawai ba ne, a’a, rayuwa ce da ta ƙunshi haƙƙoƙi, nauyi, kulawa, haƙuri, fahimtar juna da tausaya wa juna.
Gina kyakkyawar soyayya da tausayi a tsakanin ma’aurata.
A matsayinka na namiji, yana da kyau ka gina soyayya mai tsafta tsakaninka da matarka. Kada ka ɗauka cewa da zarar an yi aure, to shikenan soyayya ta ƙare. Abin takaici, a wasu gidajen da zarar an ɗaura aure, sai a ga kamar an rufe shafin soyayya gaba ɗaya.
Ɗan I love you ɗin nan ma ba za ka iya buɗe baki ka ce wa matarka ba, sai dai hantara da zare ido a cikin gida.
A halittar mata, da yawa suna jin daɗin kalaman soyayya, kulawa da nuna musu cewa ana ƙaunarsu. Sai dai kash! Galibi daga cikin wasu mazajenmu sun yi nisa da wannan fanni, kamar nuna soyayya wani abu ne da bai dace da namiji ba.
To, a haƙiƙanin gaskiya, soyayya tana daga cikin ginshiƙan zaman aure mai daɗi da ƙarko. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana nuna ƙauna da kulawa ga iyalansa.
Ya kai ɗan uwa, kada ka bari ruɗin duniya ko maganganun mutane su hana ka nuna wa iyalinka soyayya, ta hanyar magana da aikatawa a bayyane. Ka fahimci cewa nuna wa matarka soyayya ba zai rage maka daraja ko mutuncinka ba a idon ta, a maimakon haka zai ƙara kusantar da zuciyoyinku ne.
Dr. Maryam.
#Managarciya




