Shehu Kangiwa: Tuna Gwarzo Bayan Shekaru 40 Da Rasuwarsa

Alhaji Isa Kangiwa (Mutawallen Argungu) shima Allah ya wa rasuwa cikin shekara (2018) wanda shi ne Kwamishinan gidaje da muhalli lokacin gwannati Shehu Kangiwa wanda kuma ajinsu daya tun suna yara ya bayyana marigayi Kangiwa da cewa “mutum wanda ya fi kowa basira a cikin ajinsu tun suna yara.”           Lokacin rayuwanrsa, Marigayi Shehu Kangiwa ya samu nasarori da dama a rayuwarsa. A fagen ilmi jihar Sokoto wanda ta hada da jihar Kebbi da jihar Zamfara a yau duk sun shedi bude makarantu da daga darajjojin wasu zuwa manyan makarantu. Sannan yawan dalibai masu shiga makarantu sun karu, baya ga samuwar ingantuwar yanayin koyarwa da yanayi karatu ga malamai da kuma dalibai. Lokacin gwannati Shehu Kangiwa a fito da shirin gine-ginen gidajen ma’aikata da otal-otal da ofis-ofis inda aka gina Giginya Sakariya (Shehu Kangiwa Sakatariya) da gidajen Kwamishinoni na titin Sama da gidajen ma’aikata na Unguwar Bado. Sai Giginya Otal da kuma Shukura. Lokacinsa ne a aka gina gidan tarihin mai suna Wazirin Junaidu History Bureau, da kuma dakin karatu watau State Library wanda ke titin Sultan Abubakar  Sokoto da sauransu. Gwannatin Kangiwa ta  samar da hanyoyi mota manya da kanana da suka hada babban birnin jihar da sauran sassan manyan garuruwan da kauyukka.

Shehu Kangiwa: Tuna Gwarzo Bayan Shekaru 40 Da Rasuwarsa
Shehu Kangiwa

 

Daga Ahmad N. Argungu

 

Marigayi Shehu Muhammad Kangiwa, Zababben gwannan farar hula na farko na tsohuwar jihar sakkwato ya rasu ne a wani munmunan hadari mai sosa rai shekaru 40 da suka wuce. Ya rasu a sanadiyya raunin da ya samu  bayan ya fado daga saman doki lokaci da suka buga gasar wasar polo a garin Kaduna.
Hakika ba a yi wasu bayanai ko rubuce-rubuce ba na a zo a gani game da shi kansa ko ayukkansa tun bayan rasuwarsa. To da yake, bai kamata a manta da wannan jarumi ba haka kawai, musaman idan dai har abin da ake fada a cikin taken kasa abin dogaro ne “The Labour of our heros past shall never be in vain”wato “ Fadi tashi da magabatarmu suka yi ba zai taba zama banza ba.”
          Marigayi Kangiwa wanda ya rasu 17 ga nuwanba 1981 ya yi aiki a matsayinsa na gwanna ne duka natsawon shekaru biyu da wata daya da kwanaki goma sha shida, amma cikin dan wannan kankanen lokaci babu fannin  da gwannatinsa ba ta taba ba wajen aiwatar da ayukkan cigaban jiharsa.
Ranar 28 ga watan maris 1980, Lokacin da ya gabatar ka kasafin kudinsa ga ‘yan majalisar jihar Sakkwato, Kasafin da yi wa taken “kasafi na gaskiya domin mutanen karkara,” Wannan kasafi ya sa an kirkiro sabuwar ma’aikata mai suna Ma’aikatar Raya karkara. Domin tabbatar da nasarar wannan ma’aikata, Sai gwanna Kangiwa yabar ta a karkashin kulawarsa domin  ya ga cewar an samu raguwar kwararuwa mutanen karkara daga kauyuka zuwa birane. Manufar Shehu Kangiwa shi ne ya ga cewa an tallafa masu  wajen habaka ayukansu na noma da samar musu abubuwan more rayuwa da bunkasa harkokin tattalin arziki da walwarsu domin inganta rayuwar mazauna  karkara.

          A lokacin rayuwarsa, wasu na yi wa Shehu Kangiwa kallon mutum mai basira, da hange nesa da kyauta da yin haba-haba da jama’arsa. Kwarjininsa ya kara fice tare da karuwa wajen jiharsa lokaci taron gwannonin Jam’iyar NPN. A fagen siyasa kuma  takwarorinsa na kallonsa a matsayin mai dinbin hikimomi da dabarun shawo kan magoya baya musaman a fagen kanfe. Mutum ne mai sha’awar wasanin motsa jiki kamar kwallon dawaki wato Polo wadda shi ne sanadiyyar kafuwarta a Sokoto. Da yawa daga cikin  abokansa na kallonsa mutum mai kwazo da  cika alkawali. Shahararen Mawakin na Hausa Alhaji Sani Aliyu Dan dawo wanda shi shi ma Allah ya yi masa cikawa ya kan kira shi “Shehu mai fada da cikawa ne” akidar da aka rasa a wajen siyasar wannan lokaci da muke ciki.

          Lokaci da aka kawo gawar  marigayi Kangiwa zuwa Sokoto daga Kaduna, fiye da jiragen sama 25 ne suka sauka a filin saukar jiragen sama na Sokoto dauke da dubban mutane masoyansa da abokansa da ‘yan siyasa daga ciki da wajen Nijeriya domin su halarci jana’izarsa. Wannan ya nuna irin kyakkyawan zaman da Shehu Kangiwa ya yi da jama’a a ciki da wajen Nijeriya.

          Alhaji Isa Kangiwa (Mutawallen Argungu) shima Allah ya wa rasuwa cikin shekara (2018) wanda shi ne Kwamishinan gidaje da muhalli lokacin gwannati Shehu Kangiwa wanda kuma ajinsu daya tun suna yara ya bayyana marigayi Kangiwa da cewa “mutum wanda ya fi kowa basira a cikin ajinsu tun suna yara.”

          Lokacin rayuwanrsa, Marigayi Shehu Kangiwa ya samu nasarori da dama a rayuwarsa. A fagen ilmi jihar Sokoto wanda ta hada da jihar Kebbi da jihar Zamfara a yau duk sun shedi bude makarantu da daga darajjojin wasu zuwa manyan makarantu. Sannan yawan dalibai masu shiga makarantu sun karu, baya ga samuwar ingantuwar yanayin koyarwa da yanayi karatu ga malamai da kuma dalibai. Lokacin gwannati Shehu Kangiwa a fito da shirin gine-ginen gidajen ma’aikata da otal-otal da ofis-ofis inda aka gina Giginya Sakariya (Shehu Kangiwa Sakatariya) da gidajen Kwamishinoni na titin Sama da gidajen ma’aikata na Unguwar Bado. Sai Giginya Otal da kuma Shukura. Lokacinsa ne a aka gina gidan tarihin mai suna Wazirin Junaidu History Bureau, da kuma dakin karatu watau State Library wanda ke titin Sultan Abubakar  Sokoto da sauransu. Gwannatin Kangiwa ta  samar da hanyoyi mota manya da kanana da suka hada babban birnin jihar da sauran sassan manyan garuruwan da kauyukka.

          Marigayi Shehu kangawa yarasu yabar mata uku da ‘ya’ya tara. Da yake bayani kan yadda rayuwarsu ta kasance bayan rasuwar mahaifinsu, daya daga cikin ‘ya’yansa Malam Ibrahim ya koka da cewa rayuwar dai ta kasance ba dadi sai handala ga Allah. Ya ce dukkan aminan Babansu sun kaurace gidan illa kalilan daga cikinsu. Ya ce daga cikin abokan Babansu masu ziyarar gidan har yanzu akwai Kanar Dangiwa Umar (Mairitaya) da Sanata Garba illah Gada da Injiniya Murtala Zauro da kuma marigayi Alh. Umaru Ali Shimkafi (Marafan Sokoto)’

 Ana iya samun Ahmad N. Argungu ta Adareshinsa na yanar gizo tanimunanabo@gmail.com