Shagari Baya Bukatar Gwamnatin Sakkwato Ta Sake Gina Masa Gidansa Da Ya Kone Sai Dai

Shagari Baya Bukatar Gwamnatin Sakkwato Ta Sake Gina Masa Gidansa Da Ya Kone Sai Dai

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya ba da umarnin sake gina gidan tsahon shugaban kasar Nijeriya Alhaji Shehu Aliyu Shagari wanda ya kone a kwanakkin da suka gabata.

Gwamnan ya ba da umarnin ne jim kadan bayan ya ziyarci gidan domin ganewa idonsa irin hasarar da aka yi inda wutar ta lakume.

Ya ce gidan yana da matukar muhimmanci gare su, zaman gidan shugaban kasa na farko ne  da aka zaba a dimukuradiyar Nijeriya.

Wannan yunkurin abu ne mai kyau a sake gina gidan tsohon shugaban kasa da ya kone, amma in da gizo ke saka wanda za a sake ginawa gidan haka yake bukata ko akwai abin da gidan zai yi masa in an gyara.

Tsohon shugaban kasa Shehu Aliyu Shagari ya bar duniya baya bukatar a gyara masa gidan da iyalansa ba su cikinsa amma yana bukatar gwamnati ta sake fasalin gidan a mayar da shi makarantar Islamiyya ko cibiyar nazarin addini ko cibiyar taimakon marayu domin samar da lada mai gudana gare shi. 

Akwai bukatar gwamnatin Sakkwato ta sauya tunaninta ga sake gina gida, mutane su rika kwana ciki kawai bayan mai gidan yana bukatar sadaka mai gudana da abin da al'umma za su rika tunawa da shi saboda gudunmuwar da ya bayar ga cigaban kasa da jihar Sakkwato.