Saudiya ƙasa ce mai kirki a wurinmu----Buhari

Saudiya ƙasa ce mai kirki a wurinmu----Buhari
Saudiya ƙasa ce mai kirki a wurinmu----Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Talata, ya karbi bakwancin Ministan Harkokin waje na ƙasar Saudi Arabia a Fadar Gwamnati Abuja, ya bayyana cewa Kasar dake da Arzikin Man fetur ta kasance mai nuna halin kirki ga Najeriya. 
Daya karbi bakwancin Mai Girma Yarima Faisal Farhan Al-Saud, Shugaban ƙasar ya ce, duba da yawan al'umman da Najeriya ke da shi da giɓin aiyukan cigaba, ƙasar tana buƙatar harajin kuɗin  Mai, wanda shi ne gishikin tattalin arziki, ita Saudi Arabia abokiya ce  gari gare mu, inda da yawan lokaci ƙasar kan sadaukar da  yawan Mai don ba mu zarafi ɓatar da namu,"

Shugaba Buhari ya nuni da cewa, Dangantaka dake tsakanin ƙasashen biyu yana da karfi sosai, "kuma ya samu asali ne a lokacin baya, a  fannonin bukatun kai dana ƙasa."
Shugaba Buhari ya kara da cewa "Dangantakar tanada tsawo kuma Juriya," 
Yarima Al-Saud ya mika sakon gaisuwa daga Sarki Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, ya ce Masarautan tana farin cikin dangantaka da Najeriya, "wanda ya samu asali Shekaru 61 da ya shuɗe, kuma muna da bukatar kara karfafa shi zuwa gaba."
Kasashen biyu, ya ce, suna da kyakkyawan al'amura a fannin tattalin arziki da Siyasa, ba kawai tsakanin shugaban ni ya tsaya ba, a a har ga mutanen kasashen.

"akwai abubuwa da dama da haryanzu  zamu iya yin su tare," Cewar Yariman.