Sarkin Musulmi ya baiwa Gwamnan Bauchi da Gombe da Yari da wasu 12 Sarauta

Sarkin Musulmi ya baiwa Gwamnan Bauchi da Gombe da Yari da wasu 12 Sarauta

Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya baiwa Gwamna Bauchi Alhaji Bala Muhammad sarautar Kauran Daular Usmaniyya da Gwamnan Gombe Alhaji Muhammad Yahaya Inuwa Dan Amanan Daular Usamaniya.

A wata takarda da sakataren fadar sarkin musulmi Alhaji Sa’idu Muhammadu Maccido ya sanyawa hannu aka baiwa manema labarai ta nuna mutum 15 ne Sarkin musulmi ya baiwa sarautun daban-daban ciki da wajen Sakkwato.

An baiwa tsohon ministan sadarwa Shaikh Ali Isah Pantami sarautar Majidadin Daular Usmaniya, sai tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari, Marafan Sakkwato.

Sanannen malamin addini a jiha Farfesa Mansur Ibrahim an ba shi Dan masanin Sakkwato, Farfesa Ishaq Oloyede shugaba kuma rijistaran JAMB ne Kulliyan Sakkwato.

Sarkin ya baiwa babban dansa Abubakar Abukar Sadik(Amir) sarautar Sarkin Dawakin Tsakar Gida, sai Alhaji Bello Ibrahim Gusau Sarkin Malaman Sakkwato, da sauransu.

Masarautar Sarkin musulmi ta yi fatan alheri ga wadanda ta baiwa sarautun kuma za ta sanar da su ranar da za a yi masu nadi.