Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharrami

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharrami

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Muharram 1447 daga gobe Laraba 29 ga watan Zulhijja 1446  wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yuli 2025.
Sarkin Musulmi ya ba da Umurnin ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin baiwa majalisar sarkin musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu aka baiwa manema labarai.
Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanarwa hakimi ko uban kasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi.
Ya roki Allah ya kawowa Nijeriya zaman lafiya da cigaba mai dorewa.
Watan sabuwar Shekara kenan na addinin musulunci zai soma.