Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Lahadi ta zama 1 ga watan sabuwar shekara

Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Lahadi ta zama 1 ga watan sabuwar shekara
 

Mai martaba sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya ayyana ranar Lahadi ta zama 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1446 bayan hijira.

Sarkin Musulmi ya aminta da rahotanni da aka ba shi na rashin ganin jinjirin watan Muharram.
Shugaban kwamitin da ke baiwa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini Farfesa Sambo Wali Junaid ya ce kwamitinsu hadin guiwa da kwamitin ganin waata na Nijeriya sun tabbatar da ba a samu ganin watan Muharram na shekarar 1446 a ranar Jumu'a, abin da ke nuna ranar Assabar za ta zama 30 ga watan Zulhijja na shekarar 1445.
Ya ce kan haka Sarkin musulmi ya aminta da rahoton ya kuma ayyana Lahadi ta zama 1 ga Muharram.
Sarkin musulmi ya roki jama'a su cigaba da yi wa kasa addu'ar zaman lafiya da samun cigaba a kasa baki daya.